Shugabar Matan Jam iyyar APC ta kasa Dr Mrs Mary Alile ta yi kira ga matasa da su guji aikata abbenda ka iya hargitsa kasar nan a yayinda suke fafutukar neman yancin su ta hanyar zangaza. Tace zanga zangar.
Shugabar Matan tayi kira ga matasan dake zanga zangar cire tallafin mai da kuma rashin tsaro daya addabi kasar musamman Arewacin Najeriya dasu yi amfani da tunani da hikima domin gujewa abunda zai iya jefa kasar cikin mawuyacin hali. Tace tattaunawa da gwamnati itace mafita ta kuma yi gargadi da irin halinda kasar ka iya fadawa akan harkokin tsaro suka Kara tabarbarewa.
Dr. Mary tace Najeriya na cikin wani mawuyacin hali a bangeren tsaro gwamnati na yin iya kokarinta wajen shawo kan al,ammurran don haka Ina mai amfani da wannan damar wajen kira ga matasa da akai zuciya nesa a guji bannata dukiyar kasa data al, umma, a guji zubarda jini da kuma ci ko bannata dukiyar al, umma mu sani Allah baya barin hakin wani kan wani.
Dr. Mary ta kara da cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dama jam, iyyar APC a shirye suke su zauna da matasan domin Jin korafe korafen su da kuma samarda mafita tayi kira da a guje jefar Najeriya cikin kuncin yaki, ko rashin tsaro kamar yadda ya auku a wasu kasashen ketare kamar kasar Japan, Faransa da sauransu.
Tags
Hausa