Daga Marafa Zuwa Marafa

Alhaji Umaru Shinkafi OFR, Marafan Sakkwato, na daga cikin fitattun shugabanni, dattawa da kuma 'yan siyasar da Najeriya ta taba samarwa. Ya kasance gogaggen lauya kuma fitaccen jami’in dan sanda mai hangen nesa da kwarewa ta musamman.

A shekarar 1979, a karkashin gwamnatin Shugaba Shehu Shagari, an nada shi shugaban Hukumar Tsaro ta Kasa (NSO), wadda a wancan lokaci ita ce babbar cibiyar leken asiri ta Najeriya. Daga baya kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa hukumomin DSS, NIA da DMI, bayan kwamitin da ya jagoranta ya gabatar da shawarwarin da gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta aiwatar.

A siyasa kuwa, Marafan ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NRC a shekarar 1992, amma ya sha kaye da tazarar kuri’u kadan ga Alhaji Adamu Ciroma, Madakin Fika kuma tsohon minista a gwamnatin Shehu Shagari.

Na samu babbar dama da gagarumar karramawa ta kasancewa kusa da Marafan, wanda ya dauke ni tamkar dansa fiye da kasancewa almajirinsa a siyasa kawai. Bayan mahaifina marigayi Cif Remilekun Fani-Kayode ya gabatar da ni gare shi lokacin da aka dawo da harkokin siyasa a shekarar 1990, Marafan ya bude min kofar shiga siyasa.

Shi da marigayi Dr. Hameed Kusamotu, tsohon shugaban jam’iyyar NRC, tare da Janar Halilu Akilu, sun kasance wadanda suka koyar da ni, suka jagorance ni kuma suka ba ni kariya a shekarun farko na rayuwar siyasa. A shekarar 1992 kuma an nada ni mataimaki na musamman ga Marafan a yakin neman zabensa, tare da zama kakakin kungiyar yakin neman zabensa ta Choice ’92.

Wannan wata karramawa ce da har yanzu nake alfahari da ita fiye da komai a rayuwata.

Abin bakin ciki, Marafan ya rasu a shekarar 2016, lamarin da ya sa sarautar ta kasance babu mai rike da ita na tsawon lokaci. Sai dai na yi matukar farin ciki lokacin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya nada Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin sabon Marafan Sakkwato a shekarar 2024.

Sanata Yari ya kasance kusa da marigayi Marafan sosai, daya daga cikin wadanda ya fi bai wa kulawa da tarbiyya, sannan kuma surukinsa ne. A ganina babu wanda ya fi cancanta da wannan matsayi mai daraja fiye da shi.

Ina addu’ar Allah Ya ba sabon Marafan hikima, kariya da jagoranci domin ya ci gaba da gina kyakkyawan tarihin da magabacinsa ya bari.

Marigayi Alhaji Umaru Shinkafi ya nuna jagoranci mai nagarta da hangen nesa. Fiye da yawancin shugabannin siyasa da Najeriya ta taba yi, ya taka muhimmiyar rawa wajen karfafa alaka tsakanin Arewacin Najeriya da Kudu maso Yamma. Ya fahimci cewa hadin kai da zaman lafiyar kasa suna rataye ne a kan irin wannan zumunci, kuma ya sadaukar da kansa wajen gina wannan gada ta fahimtar juna.

Saboda haka ne ya samu karbuwa da kauna daga al’ummomi daban-daban a fadin kasar nan.

Ina da yakinin cewa Sanata Abdul’aziz Yari zai ci gaba da wannan kyakkyawan aiki tare da gina kan ginshikan da marigayi Marafan ya kafa.

A matsayina na Sadaukin Shinkafi, sarautar da Mai Martaba Sarkin Shinkafi Alhaji Mohammed Makwashe ya ba ni a shekarar 2020, ina yi wa sabon Marafan fatan alheri tare da tabbatar masa da cikakken goyon baya da zumunci.

Alakarmu a yau ta wuce siyasa ko kasancewa a jam’iyya guda. Ta koma alakar yan uwantaka da gado mai tushe a cikin martabar masarautun Daular Usmaniyya.

Ya dan uwana, ina yi maka fatan alheri a wannan babban nauyi da ka dauka. Duk lokacin da na ji maganganunka ko na ga ayyukanka, sai na tuna da marigayi Marafan Sokoto, wanda mu biyun muka yi matukar kauna da girmamawa.

Allah Ya ba ka nasara a wannan sabon matsayi da kuma dukkan ayyukan da ke gabanka.

Allah Ya albarkace ka, Ya albarkaci jama’a, shugabanni da sarakunan jihar Zamfara, sannan Ya albarkaci kasarmu Najeriya.

Salam.

— Cif Femi Fani-Kayode Zababben Jakadan Najeriya A Afrika ta Kudu, Sadaukin Shinkafi, Tsohon Ministan Al,adu kuma Tsohon Ministan Safarar Jiragen Sama. Wakilin Dokan Potiskum Lauya ne kuma dan siyasa.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post