Shugabar Matan Jam iyyar APC ta kasa Dr Mrs Mary Alile ta sauka Sokoto birnin Shehu domin Kaddamarda shirinta mai taken Project 774-Explode a Jahar.
Za,a Kaddamarda wannan gagarumin shirin a garin na Sokoto gobe alhamis 11 ga watan Yuli , inda matar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wato Senator Oluremi Tinubu zata kasance babbar bakuwa ta musamman.
Taron an hadashine da zimmar tallafawa mata Yara kanana Yan shekaru 18- 35 dakeda muradin shiga siyasa da Jagoranci da kuma kwakkwaran ilmantarwa akan harkokin siyasa da kuma basu taimakon gaggawa da zimmar cimma wannan manufa.
An fara kaddamarda taron ne a Jahar Benue a ranar 29 ga watan Juli 2024 inda aka tallafawa yara matan da makuddan kudade har Naira 500,000 ko wacce domin sama masu abun dogaro da kai, hadi da tsare tsare da shirye shiryenda zasu tallafa masu wajen samun cikakken ilimin kasuwanci, siyasa dama harkokin yau da kullum.
Babban bako na musamman Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto shine ya dauki nauyin wannan gagarumin taro inda mai dakinsa Hajiya Fatima Ahmed Aliyu zata kasance mai masaukin Baki.
Haka zalika Gwamnan Jahar Sokoto Alhaji Ahmed Aliyu ne ya dauki nauyin wannan gagarumin taro inda za,a zagulo hazikan yan mata daga kananan hukumomin Jahar a tallafa masu a Kuma saka su a tsarin Jagoranci da kuma sanin makamar aiki a bangaren siyasa da madafun Iko.
Wannan shirin na Dr. Mrs. Mary Alile an kudurta shine da zimmar zakulo yammata daga shekaru 18 zuwa 35 domin tallafa masu da kuma basu jagoranci akan harkokin siyasa.
Babu shakka wannan yunkurin zai taimaka matuka wajen bunkasa yawan mata a harkokin siyasa a Najeriya ya kuma bawa matan damar shiga a dama dasu akan harkokin.
📸 CAPACITY MEDIA HAUSA
Tags
Hausa