Shugabar Matan Jam,iyyar APC Jakadiyar Sabunta Zaton Alkhairi

A daidai lokacinda zaben gwamnoni a jahohin Edo da Ondo ke kara matsowa, CAPACITY MEDIA mujiya mai hangen nesa tayi ninkaya inda ta zakulo maku gagarumar gudunmawar da shugabar matan jam,iyyar ta APC ke bayarwa domin cimma nasara a wudannan zabubbukan da za,a gudanar a wannan shekarar ta 2024.

Dr. Mrs. Mary Alile na hawa karagar mulki a matsayinta na shugabar matan jam,iyyar ta APC ta dage damtse tare da jan ragamar matan jam, iyyar inda ta gwangwaje hazikan mata 18 a matsayin masu taimakawa na musamman a jahohin Edo da Ondo. Wannan wani yunkuri ne na yada manufa da kuma wayarda kan al,umma akan ayukkan raya kasa da shugaban kasa Tinubu Bola Ahmed Tinubu keyi wajen sabunta zato na alkhairi, da kuma cimma nasarar jam,iyyar a zaben 2024. 

Wani namijin kokarinda shugabar matar tayi domin cimma nasarar jam,iyyar shine hada kan kungiyoyin mata masu zaman kansu dake da rijista a jam,iyya a karkashin ofishin shugabar matan jam,iyyar. Kungiyar mai suna *ALLIANCE OF ALL APC WOMEN SUPPORT GROUPS:* Wudannan kungiyoyin  dake da rassa a sassa dabban dabban na kasa baki daya na samu gudumawar gaggawa, fadakarwa, ilmantarwa da kuma shawarwari hadi da tallafawa domin cimma nasara a zabuka masu zuwa, musamman a jahohin Edo da Ondo. 

A cikin watannni hudu Dr. Mrs. Mary Alile ta kawowa jam,iyya ci gaba da ya hada da tallafawa, fadakarwa da wayarda hadin kan mata da kuma wayarda kan al,umma akan manufofi da ayukkan ci gaban kasa a Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post