Shin Israila ta Wofantarda Yancinta na Zama Kasa mai Cikakken Yanci ? Femi Fani Kayode Sadaukin Shinkafi

A wani faifan bidiyo dana wallafa a shafi na X ya nuna hotunan wasu fitsararrren Bayahude na ikirarin cewa kowanne balarabe dake zirin Gaza makiyin Israila ne kuma babu abunda ya dace dasu face kisa. Irin wannan bidiyo na nuni ne da cewa yanzu kasar Israila ta zamo kasar shedanun mutane da hudubar shedan ta riga taci karfinsu. 


Mutumenda ke cikin bidiyon mai suna Eliyahu Yossian wanda tsohon sojan kasar Israila ne wanda ke magana kwatankwacin yadda yahudawa kakanninsa sukayi shekaru 2000 da suka gabata lokacinda suka giciye Yesu Almasihu mai ceto tare da ikirarin cewa sun kashe Yesu Almasihu kuma sun dauki alhakin yin haka. Cikin izgili har cewa suke

" jininshi na a hannun mu, damu da yayanmu".

Wudanda basu kalli wannan mummunan bidiyon ba zasu iya kallonshi a sashen sada zumunta na dake manhajar X da taken (@realFFK) ko kuma a @intifada. 

Idan ma har wannan haukan da rashin imanin bai isa ya harzuka ku ba to ku saurarin kalaman wani dan uwansa maridi, ja,iri mahaukaci.

Wannan shi kuma sojan Kasar Israila ne, daya dawo daga zirin Gaza yana murmushi cike da annashuwa yana cewa. 

" Muna neman jinjirai ne mu kashe, na kashe karamar yarinya yar misalin shekaru 12 amma jinjiri nakeson in kashe".

Wudanda ke ganin cewa wannan ba gaskiya bane zasu iya ganewa Kansu a sashina na manhajar X a @realFFK ko a @tparsi da @Khaledyoursy22. 

Idan har mutun na bukatar karin bayani akan me dokar Shari,ar Ingila ke nufi da cutar zuci ko kuma abunda littafin Bayibul ke nufi da ruhi mara tsarki to babu shakka wudannan mutanen guda biyu zasu nuna maka me ake nufi. 

Abun bakin ciki anan shine wannan shine tunanin mafi yawancin yahudawa zayonawa. 

Musamman yan jam,iyya mai mulkin Israila, jam,iyyar Likud da majalisar dokokin kasar ( the Knesset) dama jam,ian leken asiri na ( Mossad da Shin Bet) dama mafi yawancin sojojin Israila.


Ayi man uzuri in bada wasu misalai akan irin wannan izigalancin. 

Falasdinawa mata da maza da sojojin Israila ke kamawa suyi masu tsirara tare da yi masu fitsari da tozartasu da wulakantasu a bainar jama,a. 

Kai har wudanda suka mutu ma basu tsira ba, sojojin Israila na binsu har makabarta su wulakanta gawarwakinsu tare da cire wasu sassa na jikinsu su aika kasar Israila inda ake sayarwa ta kasuwannin bayan fage. 

A yanzu bazanyi magana akan irin fyadenda sojan kasar Israila keyiwa Falasdinawa mata da maza ba da yadda suke luwadi da su da karfin tsiya. 

Ba kuma zanyi magana akan yadda sojan kasar Israila ke amfani da haramtattun makaman phosphorus ba suna kai hari a zirin Gaza ba tun daga 7 ga watan Oktoba na 2023. 

Ba kuma zanyi magana akan yadda yahudawa ke kona kananan yara ba da wudannan haramtaccin bamabaman ba da yadda wudanda basu mutu ba ke fama da matsananciyar azaba kafin su mutu ba. 

Na san hakan, saboda naga bidiyoyin dake nuna haka a wajaje dabban dabban, saida bazan iya saka wudannan bidiyon ba saboda tsananin rashin imanin da ake nunawa dan Adam a ciki. 

Mafi yawancin su aboki na mai Martaba Abdullah Abu Sawesh wato jakadan Falasdin a Najeriya ne ke turo man su. 

Bayan na kalli wudannan bidiyon nayi matukar nadama da zubarda hawaye, inda har nake gayawa jakadan Falasdinu cewa inada yakinin duk wasu shedanu da sukayo kaura daga wutar jahannama tabbas sun koma kasar Israila ne. 

Wannan kadan ne daga irin rashin imani, da zalunci, kisan kiyashi da kisan kare dangi da kasar Israila ke aikatawa a zirin Gaza. Tabbas abun bakin ciki ne da rikitarwa. 

Suna bi tare da kashe mata da kananan yara kaman suna kashe kifi a cikin koma. 

Amma duk da haka, kasashen duniya sunyi shiru suna kallon irin wannan rashin mutumcin da rashin adalcin na aukuwa ba tare da hukunta kowa ba. 

Tabbas wannan ba karamin abun bakin ciki bane ga bil Adam, inda daya daga cikin  kasashe mafi karfin soja a duniya ke gallazawa fararen hula azaba wudanda basuji ba basu ganiba .

Amma dukda irin wannan abun kunyan, Yahudawa zayonawa sai murna suke suna ikirarin samun nasara akan mata da kananan yara. Tir

Abunda basu saniba shine da sannu wannan murnar zata koma ciki. 

Na fadi haka ne saboda a halin yanzu mutane da yawa sun fara aminta da wudanda a da can baya sukayi kwankwanton idan har kasar Israila ta cancanci yancin zama kasa ta kanta. 

Sannan kuma tunanin cewa ya kamata a shafe kasar ta Israila daga bayan kasa ya fara samun goyon baya daga milyoyin mutane. 

Saboda shirme, hauka da rashin imanin Firamisnta Shedanyahi da irin kishin jini da sojojinsa ke nunawa hadi da rashin imanin da suke nunawa karara wajen yiwa larabawan Gaza kisan gilla da kisan kare dangi a idon duniya yasa mutane da yawa sun fara tunani irin na Hitla wanda yace babban maganin matsalar Yahudu shine a shafesu daga bayan duniya a lokacin duniya tayi caa akan shi. Yau gashi yahudawa sun fito karara sun nuna aniyarsu ta shafe Falasdinawa daga doron kasa. Wannan ya nuna cewa kungiyinda ake gani sun kakkausa harshe kamar su Hizbullah, Hamas wajen kiran cewa ya kamata a kawarda kasar ta Israila daga bayan kasa sunada Hujja da dalili mai karfi. 

Bari in Nanata. 

Ni inada yakinin cewa yarjejeniyar Oslo wacce ta nemi a kafa kasashe guda biyu a yankin Falasdinu itace kawai mafita, kasa daya ta larabawa, daya ta Yahudawa.  Ban yarda da cewa a shafe Israila daga bayan kasa ba ban kuma yarda da cewa hakan abune mai yiyuwa ba. Amma a hakikanin gaskiya idan na kalli irin rashin imanin da yahudawa ke aikatawa a zirin Gaza hakan na sa inji ya dace in sauya tunani na. 

Abun mafi muni ma shine a halin yanzu mafi yawancin mutane na ganin cewa babu wani banbanci tsakanin yahudawa da zayonawa, a tasu fahimtar duk wani bayahude makiyin larabawa da musulunci ne kai ma makiyin bil Adam ne.

Abun bakin ciki wannan itace irin gudunmawar da Shedanyahu ya bawa kasarsa ta Israila. 

Ya janyowa jinsinsa na yahudawa bakin jini fiye da duk wani shugaba a cikin shekaru 6000 na tarihin Yahudu. 

Yiman Uzuri indanyi tsokaci tare da bada misalin irin mummunan tunanin mutane da suka zagaye gwamnatin Shetanyahu. 

Kwanaki kadan da suka wuce censored Men sun buga wani hasashe dake bayyana irin kalar mutane da Natanyahu ya cika gwamnatinsa dasu. 

Sun rubuta. 

" Benjamin Natanyahu na da mutane kala kala a cikin gwamnatinsa amma daga cikinsu mutane biyu sunyi fice fiye da sauran. 

Wudannan mutanen sune Itama Ben-Gvir ( Ministan tsaro) da Bezale Yoel Smotich ( Ministan kudi)


Kafin muci gaba zanso ku sanda cewa wudannan mutanen guda biyu Natanyahu ne da kanshi ya nada su a wudannan mukaman. 

Ci gaban bayanin. 

Itama Ben-Gvir:

 *-* ya aminata da cewa al,adar yahudawa ta tofawa kiristoci da malaman su yawu al,ada ce mai kyau bai kuma kamata a hukunta masu yin hakan ba. 

- Yana da yakinin cewa bayahude yafi duk wani mutum muhimmanci a bayan kasa. 

Ya nuna hakan a lokacinda yace. 

"Yancina dani da matata da yayana na mu zagaya zirin Gaza a duk lokacinda mukeso yafi duk wani yanci na larabawa muhimmanci".

- Yasha Ciro bindiga yayi ikirarin cewa zai kashe larabawa masu aikiba matsayin masu nuna wajen ajiye motoci a Tel Aviv. 

- Yayi kaurin sunan rataya hoton Baruch Goldstein a bangon gida da ofishin sa. 

Shin ko kunsan waye Baruch Goldstein?

Baruch Goldstein ba Amurken Bayahude ne dan ta,adda daya kai harin ta,addancinda ya kashe Falasdinawa 29 dake dakin ibada a birnin Hebron a shekarar 1994. 

- Watan June daya gabata 2023 ya shiga masallacin Kudus inda ya ayyana cewa Israila ce keda cikakken iko da zimmar tada kayar baya. 

An sameshi da wudannan laifukan. 

* Tursasawa akan wariyar launin Fata da kabilanci. 

* Barnata kayan larabawa. 

* Mallakar takardu bugun kungiyoyin ta,addanci. 

* Goyon bayan ta,addanci da yan ta,adda. 

Yanzu da kunsan waye Ministan tsaro na Israila bari kuma kusan wanene ministan kudin.  

Bezalel Smotrich:

A shekarar 2016 yayi bayani inda yace bai kamata matan yahudawa masu juna biyu su ringa ziyarar asibiti daya da matan larabawa masu juna biyu ba.

A watan Feburairu na 2023 yace yana goyon bayan a shafe kasar Falasdin daga bayan kasa. 

* watan Mayu 2023 yace babu wani abu kamar Falasdin, kuma babu wani abu kamar Falasdinawa. 

- Watan Mayu 2023, Smotrich ya ziyarci kasar Faransa inda ya nuna taswirar Gagarumar kasar Israila kafin yace. 

Gagarumar kasar Israila ta hada da:

* Ilahirin Falasdin
* Ilahirin Kasar Jordan
* Yankin kasar Irak
* Yankin kasar Lebanon
* Yankin kasar Siriya
* Yankin kasar Masar
* Yankin kasar Turkiyya
* Yankin kasar Saudiyya. 

Wudannan sune yan gaban goshin Natanyahu. 

Meyasa?

Saboda duk wata ta,asa da suka aikata, ko aika aika da suka aikata Natanyahu zai karesu, ba kuma zaiyi wani yunkurin tsigesu daga mukaminsu ba. 

Ina fatan wannan post din zai baku cikakken haske akan irin mummunar aniyar gwamnatin Israila. 

Wannan wata muhimmin gudumawa ce daga shafin @censoredMen kuma na yabawa irin namijin kokarinda suke yi. 

Wannan wata manuniya ce dake dasa alamar tambaya shin akwai wata gwamnati data tara jerin kwararrin yan ta,adda, mashaya jini kamar gwamnatin Israila a duk fadin duniya?

Shin anya wannan ba shi bane irin tunanin Adolf Hitler daya bayyana a cikin littafinsa mai suna (Mein Kampf) wato Gwagwarmaya ta? Wanda ya so ya ja kunnen duniya dangane da hatsarinda ke tattare da sakewa yahudawa mara?

A hakikanin gaskiya na tsani Hitla, na kuma tsani irin tunanin shi da duk wata akida tashi dama tunanin shi na cewa jinsin shi na Aryan yafi sauran mutane. 


Ina kuma mai yin Allah wadai ga duk wani abun wulakanci ta keta Hakim dan Adam da sukayiwa Yahudawa, Slabiyawa, yan luwadi dama sauransu. 

Amma abunda nake tambaya shine shin ko Hitla ya tsinkayo irin mummunan halinda yahudawa keda burin saka duniya ne tun wudancan shekarun da suka gabata?

Kamar dai yadda Bayibul ya nuna labarin Haman wanda shima kamar Hitla yayi burin yayi wa Yahudawa kisan kare dangi, ya kwace kasarsu da dukiyoyinsu haka yau Yahudawa ke nunawa duniya bukatarsu ta yiwa Falasdinawa kisan kare dangi su mallake filayensu da dukiyiyinsu. 

Abun mamaki anan shine mutane da a jiya ke fama da matsalar mulkin mallaka, ake masu kisan kiyashi yau sune ke yiwa wasu mulkin mallaka da kisan kiyashi. 

Shin akwai wani banbanci tsakanin yahudawa zayonawa a karkashin mulkin Natanyahu da sauran azzaluman da suka gabata kaman su Hitla,Goebbels, Himmler, Gorin da sauransu?

Wudancan da suka gabata sunyi sanadiyyar mutuwar mutum milyan 50 a yakin duniya na biyu, wudannan yahudawa na barazanar sanadiyyar mutuwar bilyoyin mutane a lokacinda yakin duniya na uku zai kare. 

Shin meye banbanci tsakaninsu, shin dukansu daya ne?

Zamu iya kwana muna mahawara akan wannan amma karamar yarinyarda ta rasa iyayenta, kakanninta, da sauran yan uwanta kafin akayi mata fyade aka barta baci ba sha ba hanyar magani bazata taba gane meye banbanci tsakanin yahudawan zayonawa ba da Hitla da mutanenshi. 

Zata kuma rantse ta kuma gayawa duk wani wanda ya bata damar magana cewa da Nazi yan Jamus lokacin Hitla da Yahudawa zayonawa karkashi Natanyahu duk uwarsu daya ubansu daya, iya banbancinsu shine yahudawa zayonawa sun mallaki kasar Amurka da sauran kasashen Turai. 

Shi yasa ba abun mamaki bane da gwamnatin Afrika ta nemi cewa kotun hukuntar laifukan yaki ta binciki kasar Israila akan laifulan kisan kare dangi a zirin Gaza?

Satinda ya gabata na rubuta wata budaddiyar wasika zuwa ga shedanyahu inda a cikin ta nace shedanyahu yana fama da tabin hankali kuma yana bukatar maganin gaggawa. 

Na cimma wannan matsayin ne sakamakon wani bincike mai zurfi danyi sai kuma gashi wani shaharraren mai shirya fina finai a masana,ntar Hollywood dake kasar Amurka Roger Stone inda yace yakai ziyara ta musamman zuwa ga shedanyahu, a nasa fadar irin tsare tsare da manufofinda shedanyahun ya gabatarmasa sunsa ya yanke shawarar cewa shadenyahu bashida isassshen hankali. 

Bayanin Stone da kuma sanarwarda @Sensoredmen suka fitar ta nuna cewa babu shakka shedanyahu na fama da matsanancin tabin hankali. 

Sam ba abunda ya shalleshi, iya tunaninsa shine kasarsa ta mallaki makaman Nukiliya da zai iya bada umurnin a buga wa ko wace kasa a kowane lokaci tabbas wannan abun tsoro ne. 

Tabbas dole ne a dauki mataki mai tsanani akan shedanyahu, sannan kuma tilas ne yahudawan Israila su dage da ganin an tsagaita wuta a yakinda Israila keyi a zirin Gaza, sannan a cire shi daga mulki kana a masa hukunci mai tsanani ko a mikawa kotun laifukan yaki ta masa hukunci akan laifin kisan kiyashi da kare dangi a zirin Gaza. Wannan itace kawai mafita. 

Tabbas jiya duniya ta dage damtse ta taimaki yahudawa a lokacinda Hitla yaso yayi masu kisan kare dangi. 

Yau ya dace duniya ta mike ta dage damtse ta taimaki Falasdinawa. 

Lokacin ne kawai ake jira. 

Kasar Israila yar gatan duniya yau ta zamo abar kyamar kowa. 

Kaico da mummunan karshe. 

Femi Fani Kayode Sadaukin Shinkafi ya rubuta. 

Mohammed Bello Doka ya fassara daga Turanci zuwa Hausa.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post