Budaddiyar Wasika Zuwa ga Firaministan Israila Bibi Natenyahu daga Cif Femi Fani Kayode Sadaukin Shinkafi

Ina mai fatan cewa wannan wasikar ta sameka cikin koshin lafiya da nishadi duk da irin kalubalenda kai da kasarka kuke fuskanta a daidai wannan lokacin. 

Zan fara da baka hakuri akan wannan zabin nawa na aika maka budaddiyar wasika. Bani da wata hanya da zan aika maka wannan wasikar in kuma tabbatar ta sameka. Sannan banida tabbacin cewa idan na aika wannan wasikar zuwa ofishinka dake Tel Aviv wasikar zata wuce teburin shugaban ma,aikanta ballantana ta sameka. 

Duba da irin halinda gabas ta tsakiya ta samu kanta a ciki, dama kasarka ta Israila na ga ya dace kaji wasu baituka na gaskiya duk dacinta, ina kuma fatan cewa jakadan ka a kasarmu ta Najeriya, mai martaba Michael Freeman, tare da sauran yan leken asirin Ku, da sauran yan anshin shatanku a nan kasar zasu sanar dakai dangane da wannan wasikar.


Sai bayanin dalla dalla.

Ranka yadade, ina neman izininka domin shaida maka cewa ina matukar girmama kujerarka amma bana girmama ka, kuma bana goyon bayanka. 

Ka kasance wata mummunar kadara data fadawa kasarka tun lokacinda aka kafa ta a 1948 saboda haka bazan kiraka da Firaminista ba sabanin haka zan kiraka da bakin waken lokacin mu, kuma makashin kananan yara. 

Burin ka a fili yake na ka sheke ilahirin al,ummar Gaza, kayi masu kisan kiyashi da kisan kare dangi, wannan shine makasudin kisan sama da Falasdinawa 26,000 wudanda basuji ba basu gani ba. ( wannan alkalumman sunyi daidai da fiye da kashi 1% cikin 100% na al,ummar Gaza) a ciki akwai yan jarida 97 ( a cikinsu harda Samer Abu Daqqa na Al Jazeera) da kuma Israilawa 3 da suka gudo daga hannun Hamas suna neman mafaka. 

Daga cikin Falasdinawa 26,000 kimanin 10,000 yara ne kanana, 6,400 mata ne da basuji ba basu gani ba, daga cikin wudannan 26,000 da kuka halaka an tsinci sama da 20,000 warwatse akan rusashshin gidaje, kimanin 6,400 kuma an samo su ne binne a karkashin kasa. 

A kalla yara 24,000 ne suka zama marayu a sanadiyyar wudannan hare haren kan mai uwa da wabi da Israila ke yi a zirin Gaza. Sama da 18,000 sun samu raunuka kashi 60% daga cikinsu kuma sun jikkata  a yayinda zirin na Gaza ke fama da matsananciyar yunwa. 

Ma,aikatan lafiyan Falasdinawa 300 ne aka kashe, a hannu daya kuma ma,aikatan jinkai na majalisar dinkin duniya 134 ne aka kashe a daidai kokacinda Falasdinawa milyan daya da dubu dari tara suka rasa muhalli, babu ruwa, ba abinci ba magani kana ba matsuguni. Haba Natenyahu.

Karka manta cewa Falasdinawa 288 ne aka kashe a gabar tekun Nil haka kuma Falasdinawa 4,570 ne kuka kama kuke azabtarwa a gidajen yari tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.


Karka manta Israila ta rusa sama da gidajen Falasdinawa 100,000, haka kuma kun harba bom a matsugunin ya gudun hijara da yayi sanadiyyar kisan dubban Falasdinawa, bazamu manta ba da yadda sojan Israila yayi amfani da bindiga mai hangen nesa ya sheke wata bafalastinuwa da yarta a cikin Coci. 

Wannan kisan na Bafalasdiniwar tabbas wani mummunan laifin yaki ne kamar yadda Fafaroma Francis ya kirashi harin ta,addanci. 

I zuwa ranar 1 ga watan nuwanba sojojin Israila sun harba bamabamai 12,000 a zirin Gaza, wudanda suke dauke da nauyin Tan 40,000 na bam, wudannan hare haren sunyi sanadiyyar rushewar sama da rabin gidajen da ke zirin Gaza. A tarihi ba,a taba samun garinda aka yiwa ruwan bamabamai ba irin yadda Israila tayiwa zirin Gaza. 

Sakamakon haka kashi 71% na mutanen Gaza na fama da mummunar yunwa, kashi 98% na fama da karancin abinci, kashi 64% na cin ciyawa, yayan itace da abincinda bai dahuba dama Wanda ya lalace domin kubuta daga matsananciyar yunwarda kasar ta Israila ta jefasu. 

A daidai lokacinda bikin kirsimati ya ke kara matsowa garin Bethlehem inda aka haifi Yesu Almasihu mai ceto yana cikin halin kakanikayi saboda hare haren Israila. Amma ko a jikinka Natanyahu kama sadaukarda rayuwar yan uwanka 130 da ake garkuwa dasu a wannan garin domin ramuwar gayya. 

Tabbas saidai wudanda basuda yaya ne ko marasa imani ne kadai bazasu tausayawa jama,ar Falasdinu ba.

Shin Mr. Natanyahu ko zaka musanta zancen Dr. Mustafa Barghouti tsohon ministan sadarwa na gwamnatin Falasdin kuma dan majalisar Falasdinawa a yanzu inda yace " babu wani mutum a Falasdin dakeda wata kima a idon Israila, ko musulmi ko Kirista. Tabbas duka duniya ta shaida cewa wannan dalilin ne yasa Israila ke kashe yan Jarida dake kawo rahoton irin wannan kisan kiyashin. 

Ba abunda muke gani daga wudannan rahotannin da yan jarida ke haskowa sai, gawarwaki, jini, da sassan jikin matattu baka jin komai daga kukan kananan yara, sai warin jini da makamantan haka. Tabbas wannan manuniya ce ga irin mummunan hali, zalunci, kisan kiyashi da kisan kare danginda Israila keyiwa Falasdinawa da basuji ba basu gani ba. 

Natanyahu kaika gayawa Falasdinawa fararen hula dasu bar arewacin Gaza su koma kudanci, kace idan sukaje can sun tsira. 

Bayan sama da mutum milyan daya daga cikin su sun yarda da zancenka sun bar Arewacin zuwa kudancin Gaza saika bisu da bamabamai ka ringa tarwatsa su Wanda yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane. 


Natanyahu a cikin wata biyu ka kashe mutane fiye da mutanenda Amurka ta kashe a mulkin mallakarda sukayiwa kasar Afghanistan na shekaru Ashirin da daya.

Ko makabartu, mutuwari baka bari ba saidai ka aika sojojin ka suka ringa harba bamabamai suna tarwatsa gawarwakin mutanenda ke kwance matacci. 

A karkashin jagorancinka kasar Israila ta zamo abunda mai sharhi Mr. Cent Uygar yace  Israila ta zamo " Kamfanin kisan kai".

Ka gayaman Bibi, taya kake iya bacci da dare ?

Gaya man wanne irin mafarki kakeyi, kuma wudanna irin ababen tashin hankali kake gani idan ka kulle idonka ?

Taya kake kallon matarka da yayanka idan gari ya waye, da kuma wace irin zuciya kake kallon ubangijinka ka kuma yi addua gare shi, da irin wannan jinin a hannayenka?

Natanyahu wai sai yaushe kishin jininka, tsanar Falasdinawa da sha,awar zubarda jininda ke damunka zasu kau?

Yaushe ne burinka na kisan kiyashi da kisan kare dangi da bautarda Falasdinawa zai kau?

Inason in gaya maka gaskiya, gaskiya mai daci, gaskiyarda mutane da yawa suka kasa gaya maka. Rashin imaninaka, rashin tausayinka, yunwar zubarda jini, rashin hangen nesa da busashshiyar zuciyarka tamkar Wanda wasu bakaken shedanu daga wutar jahanama suka shafa. 

Don haka mutane da yawa kan kiraka Natanyahu a gaban idonka amma su kiraka Shedanyahu a bayan idonka. 

Ka kasa cimma burinka na murkushe yan kungiyar Hamas saidai kisan kiyashi wa mata da kananan yara na nuni ne da karin rashin imaninka, rashin tausayi da rashin jinkai da kuma irin duniyarda kake rayuwa a ciki. 


Ka rufe kunnenka da zuciyarka dama tunaninka ka kasa ganin amfanin tsagaita wuta a yakin cin zalin da kuke a Gaza. Ka kasa ganin alfanun sasancin kasashe guda biyu. 

Bukatar zuciyarka itace kisan kiyashi, kisan gilla, zubarda jinin Falasdinawa da kuma niyyar yi masu kisan kare dangi domin ku mallake kasarsu, filayensu da zimmar kafa kasar Israila wacce akewa lakabi da greater Is real " wato Gagarumar Kasar Israila " mai iyaka da kasar Masar, da Iran. Burin kafa kasar wariyar launin fata da ta,addanci wacce ke kallon duk wani wanda ba bayahude ba a matsayin bari, jaki koma wata kaskantacciyar halitta da bata kai dan Adam ba. 

Ga dukkan alamu wannan wata makauniyar shawara ce da bazata haifa maka da mai ido ba. 

Ina mai tabbatar maka da cewa kai da irinku masu tunaninka ba komai bane face wata mummunar cuta data addabi bil Adam. 

Kaiba mai kare muradin kasar Israila bane kamar yadda kake daukar kanka kuma kake babatu, kai ba kowa bane face wani soko shashasha sanadin masifa da tashin hankali ga yahudu. 

Baka kawo wa yahudawa komai ba face kunya, tsana, yaki, da tsinuwa. Ka kasance shugaban da akafi tsana a tarihin Israila dama duniya baki daya. 

Kaiba mai kare muradin kasar Israila bane, face makashin kananan yara da mata. 

Kamar duk makasa bana shakkun cewa zaka kare a wutar jahannama ga dukkan alamu kuma zaka ja kasarka ta Israila zuwa rintsin kasan wutar jahannama. 

Dafatan ban bata maka rai ba Mr. Bibi amma dole in gaya maka gaskiya mai daci. 

Kayi man uzuri in kare wannan wasikar soyayyar da kalaman wani dan kanzaginka, a wani rahoto daya buga a shafinsa na manhajar X wanda ke nuna irin kiyayya da kin jinin wudanda ba Zayonawa ba irinku. 

Dr. Eli David, wani mai sharhi na musamman, malami, dan kasuwa, kuma daya daga cikin wudanda suka kafa kamfanin Deep Instinct Ltd wanda kafafen yada labarai suka ce shafin X dinshi na daya daga cikin shafuka 100 na X masu matukar muhimmanci inda ya saka bidiyon mata musilmai sanye da Hijabi tun daga sama har kasa suna tattakin zangazanga a birnin London.

A karkashin bidiyon yayi rubutu kamar haka:

" Wannan ba Islamabad bace, London ce sannunku da kare hakkin dan Adam"

Tabbas mun fahimci manufarshi. 

Yana zolayar Ingilawa ne wai saboda akidarsu ta kare hakkin dan Adam sun bari larabawa, musulmai sun mamaye kasarsu. 

Abunda ya manta ko yaki ya bayyana shine tabbas wannan akidar ta zama da jinsi dabban dabban ta kasar Ingila ta kawowa kasar ci gaba da wayewa dama karbuwa a duniya, inda har a yau an samu Firaminista dan kabilar Hindu, Mayon London Musulmi da kuma musulmi wanda ba bature ba a matsayin Firaministan Scotland. 

Ingila kuma nada bakar fata a matsayin ministan harkokin cikin gida, sannan kuma da ministan harkokin kasar waje wanda ya sauka nan bada dadewa ba. 

Idan akayi la,akari da irin wannan alakar shin mutum zaiyi korafin ganin matan musulmi na zangazanga a titin birnin London?

Wudanda ke ganin cewa kasar Ingila tafi dacewa da jinsi daya kawai na fararen turawa, kiristoci tabbas suna akan turbar bata, tabbas kuma Ingila ta kunyatar dasu. 

Ansa ta zuwa ga Eli wanda na buga a shafi na X nada matukar muhimmanci a wannan takardar. 

Koma menene Mr. Eli zaiyi matukar taimaka maka idan zakayi la,akari da cewa ire irenmu daba yahudawa irinku ba, sannan wudanda basu da irin akidar wariyar launin fata kamar ku ba, wudanda kuke tsana da kin jini. 

Ansa ta.  

" Tabbas inada yakinin cewa ganin dubban mata musulmai sanye da bakaken Hijabai shine mafi a,a la ga Ingilawa da Ingila. 

Kaman yadda ake cewa rayuwar yar gurguzu ne, kuma cudanyar jinsi abune da bazai kauce ba a Ingila. 

Duk da cewa wasu makakkun na zolaya wai ya kamata a mayarda sunan birnin London zuwa Londonistan idan ma aka lura hakan zai zamo abun alfahari. 

Abu daya da baka isa ka fada dangane da Musulmi ba shine sabanin halayyar turawa basuje birnin London suka kwace filayen mutane ba da karfin bindiga. Basu kuma kori yan kasa ba ta haryar kisan kiyashi domin su kafa daular addininsu ba. 

Amma wannan shine abunda kakanninka yahudawa suka aikata. 

Idan ka manta kayi man uzuri in dan yi maka darasi akan tarihin Yahudu da Yahudawa. 

Babban dalilinda yasa kaga wudannan Musulman suka baro kasashen masu dinbin tarihin shekaru aru aru, suka zo suka zauna kasashen turawa nada alaka da wata abota data kullu tsakaninsu da Ingilawa bayan kare yakin duniya na biyu. Milyoyin turawan Yahudawa bayan kare yakin duniya na biyu ne aka yiwa kwasar share aka tsallaka teku dasu zuwa kasar Falasdin inda aka saukar dasu a matsayin yan gudun Hijira a shekarar 1948, shekaru kadan wudannan Yahudawa suka mamaye kusan dukan kasar Falasdin, suka sace filayen larabawan musulmai suka koresu daga gidajen suka ce ai su sune kabilarda Allah ya zaba. Suka kafa kasa mai suna Israila kasarda aka gina kan wàriyar launin fata, yaudara da zalunci suka rinka gallazawa asalin yan kasar kamar shara. 

Suka yi ikirarin cewa Allah ne ya basu kasar da kanshi, Allahn annabi Ibrahim, Ishaka, Yakuba da sauran su. Duk da cewa wannan ikirarin ka iya zama gaskiya amma wannan ba hujja bane na kisan gilla da kisan kiyashin da suke aikatawa. 

Sannan kuma sukayi ikirarin cewa sun zauna a kasar ta Israila shekaru 2000 da suka gabata, don haka yanzu sun sake dawowa kasarsu ta gado zasu kuma yiwa duk wata kabila dake zaune a wannan yankin a cikin wudannan shekarun 2000 da suka gabata kisan kiyashi domin su karbi kasarsu ta gado. 

Maiyiyuwa da gaskene sun zauna a kasar shekaru 2000 da suka gabata amma abun dubawa shine idan akwai adalci a cikin irin wannan tunanin nasu, koma idan abune mai yiyuwa a wannan duniyar tamu. 

Abun dubawa anan ma bawai shine ko shin Tabbas wannan kasar tasu ce ba ko a,a. Abun dubawar shine wannan muguwar akidar tasu ta cewa babu wani mai damar ya zauna a wannan yankin, saidai kowa yayi masu mubayi,a ya basu waje kosu kawar dashi da karfin bindiga. 

Idan mutun ya kalli wannan badakalar sai yaga tayi kama da wani tsari na fim din India, amma abun ban haushi da takaici wannan ba fim bane, wannan shine tunani da akidar Yahudawa Zayonawa( Zionists).  

Shin ko ka fahimci inda matsalar take?

Yafi ma,ana, kuma yafi sauki ga Balaraben Falasdin wanda aka kwace masa kasa, gida, wajen zama kuma aka bautar dasu su gudo daga mulkin mallaka su zauna kasashen irinsu Ingila koma ace a birnin Londonistan ta bakinka, ko kuma wasu kasashen da suka San mutumcin dan Adam domin su gujewa irin cin kashi, kisan gilla da kisan kiyashinda Yahudawa yan share waje zauna keyi musu a kasashensu na gado. Yahudawa masu akidar cewa sune kawai zababbun Allah, amma kiristoci da musulmai ba haluttun Allah bane don haka basuda yancin samu matsuguni, Yahudawa yan share waje zauna da suka yarda da tsarin zaman lafiya na samarda kasashe biyu daya ta Yahudawa daya ta Larabawa musulmi da Kirista. Wudanda suka nace sai sun kafa Babbar kasar Israila wadda ta tashi daga Kasar Masar a gabas ta tsakiya zuwa lardin larabawa. 

Dafatan kana fahimtar karatun karara?

Israila taki amfani da hankalinta wajen kin yarda da kafa kasa mai dauke da jinsi dabban dabban sabanin akidarsu ta kafa kasar Yahudawa zallah, akan akidar wariyar jinsi, wariyar launin fata wanda yin haka zaisa bazasu zamo barazana ga zaman lafiyar duniya ba. Matakinda yasa Israila cikin mummunan hadari dake barazana ga kasar baki daya. 


Dafatan Eli da sauran yan anshin shatansa Yahudawa yan share wuri zauna , da masu goyon akidarsa ta wariyar launin fata, kin jinin musulmi da zasu fahimci karatun karara. 

Mafi muhimmaci shine kasani milyoyin mutane na ganin ka sun kuma tsaneka fiye da irin kiyayya da tsanarda kake yiwa wasu. 

Tabbas mutum yayi suna a bangaren ta,addanci, kisan kare dangi, wariyar launin fata da zubarda jini ba wani abun alfahari bane. 

Kana a yiwa mutum lakabi da mashekin mata da kananan yara babu wani abun tsana kuma mafi muni dayafi wannan. 

Tabbas amana zata cika bazata barka ba abokina Bibi ka jira sakamako nan bada dadewa ba. amana zata cika bazata barka ba abokina Bibi ka jira sakamako nan bada dadewa ba.

Bari in tunawa suka yarda da kai kuma suke ganin cewa wai mun kausasa harshe akan zargin cewa kanada burin mamaye dukan gabas ta tsakiya da zimmar gina babbar kasar Israila. 

Kuyi man uzuri domin in tunashe ka. 

Ministan kudinka, Mr. Bezalel Smotrich yayi wata jawabi was manema labarai, wanda a baynsa akwai taswirar babbar kasar Israila inda yayi wasu kalamai masu tayarda hankali kamar haka. 

" Wudanda basu saniba su sani cewa Gagarumar Kasar Israila ta hada da dukan Falasdin, dukan kasar Jordan da wasu sassa na Iraki, Lebanon, Siriya, Masar, Turkiyya da kasar Saudiyya."

Tabbas wannan ya nuna irin mummunar akidarda ke boye a zukatanku da kuke boyewa, shikesa kuke yin duk abunda kukeyi domin mamaye kasar Falasdin. 

Haka ma, ministan al,adunka Mr. Amihay Eliyahu a kwanakin nan yake cewa yakamata a bugawa zirin Gaza makamin Nukiliya da zimmar a kori duk wani Bafalasdine daga wajen ko kuma a rarraba Falasdinawa zuwa kasashe dabban dabban na duniya a 25,000 a kowace kasa. 

A nashi bangaren ministan tsaronka Mr. Itama Ben- Gvir cewa yayi babban abunda ya kamata ya shiga zirin Gaza shina tsantsagwaron bamabamai, kada kuma a bari kwayar abinci guda ta Shiga garin har sai Hamas ta saki israliawan da take garkuwa dasu. 

Sannan kuma ya raba bindigogi masu linzami ga yan ta,addan Yahudawa yan kama waje zauna tareda umurtarsu dasu kashe Falasdinawa iya son ransu. 

Babu ko shakka cewa gwamnatinka wata kungiyar mahaukata, masu kwadayin zubarda jinin larabawa musulmi da kirista ce, babu abunda yafi dacewa dasu kamar duk ka sallamesu ka kuma turasu gidan jinyar masu tabin hankali, amma shin kai kanka kanada hankakin tunanin yin hakan?

A watan Oktoba na shekarar 2023 kai da kanka kace babu wani wanda baiji ya gani ba a zirin Gaza, ka kara da cewa wannan yaki ne tsakanin yayan duhu da yayan haske. 


Kaci gaba da cewa. Muna da muradin ganin bayan wannan mugun abun daga bayan duniya. Tabbas dole ne ka tuna da  Amalek a littafinku na Biyibul kuma mun tuna da 1 Samuel 15:3 inda yace " kuje Ku kaiwa Alamalek hari, ku tarawatsa duk wani abun da suke dashi, karku raga masu Ku kashesu gaba dayansu, mata kananan yara, masu shan mono, kai harda jinjirai da rakuma da jakai duk Ku kashe kowa da komai. 

Idan wannan ba kira bane na kisan kare dangi menene shi?

Duk da  shugaban kasar Israila Mr. Isaac Herzog wanda ake gani kamar yanada hankali da sanin ya kamata ya bari giyar mulki ta rudeshi inda yake cewa kamar haka " duka kasar Falasdin ne suka kawo mana hari a 7 ga watan Oktoba, zancen fararen hula da zancen wai akwai wudanda basuji ba basu gani ba a Gaza karyace tsantsagwaron ta, meyasa basu tashi suka yaki Hamas ba, meyasa suka bari har Hamas ta kawo mana hari?

Tabbas wannan wani mahanga ce dake nuna muradin Israila na yiwa Falasdinawa kisan kare dangi, wannan bawai kawai aikata laifukan yaki bane, wata mahangace dake nuna niyyar kisan kiyashi da na kare dangi. 

Abun bakin ciki zancen bai tsaya nan ba, haka ministan albarkatun gona a gwamnatin ka  Mr. Avi Ditcher ya fada a tashar channel 12 yana mai cewa wannan yakin zai kasance Nakba a Gaza, wato wani mummunan kisan kiyashi da akayiwa Falasdinawa a shekarar 1948 inda aka kori sama da Falasdinawa 700,000 daga gidajen su tareda kwace antaya filayensu cikin kasar Israila. 

Ya kara da cewa mun riga mun kaddamarda shirin Nakba a Gaza, Nakbar Gaza. Domin babu wata hanya da za,ayi wannan yakin cikin sauki ba tareda hakan ba. Nakabar Gaza a shekarar 2023 wannan itace kawai mafitar. 

Kafin mu manta haka shima dan majalisar Israila Mr. Danny Neumann ya bada shawarar a kashe kowa da kowa a zirin Gaza, ba mace ba yaro kai har jinjiri. 


A wata hira a gidan talabijin cewa yake...

" duka Falasdinawa yan ta,adda ne, yayan karnuka dole ne mu karardasu dukansu".

Bibi tabbas zaka yarda dani cewa, dakai da duk yan majalisar ka da gwamnatin ka wani bangarene na mahaukatan azzalumai masu shaawar zubarda jini da kisan kiyashi. Tabbas ka shiga jerin gwanon azzalumai na fada a ji a tarihin duniya kamarsu Genghis Khan, Atilla the Gun, Hitla, Sarki Leopold, Joseph Stalin da Pol Pot. 

A daidai wannan lokacin zan nemi izini in kawo kalaman Dr. Sulaiman wanda limamine, Bafalasdinen Amurka kuma shugaban makarantar Yaqeen  inda ya rubuta a shafinsa na X kamar haka. 

Dubban jinjiraye ne suka rasa rayukansu, dubban jinjiraye ne binne a kasan tarin kankare na gidaje da suka rushe, dubban yara ne ke fama da matsananciyar yunwa,  duk wani yaro dake zirin Gaza yana cikin mummunan tashin hankali zamu iya barin kungiyoyin kare hakkin dan Adam suci gaba da kiragasu ko kuma mu yi hukunci ga masu aikata wannan mummunan laifi. 


Wannan zantukan na Umar kalamaine da suka taba zukatan milyoyin mutane a fadin duniya, suka kuma fito fili suka nuna ra,ayin milyoyin mutane a fadin duniyar. 

Idan har wudannan kalaman basu sanyaya zuciyarka ba, suka saka nadama tareda zubarda hawaye to babu abunda zai saka nadama, bibi kayi batan bakatantan na har abada. 

Zan kare da wudannan kalaman. 

Duba da cewa jakadarka a kasar Ingila mai martaba Tzipi Hotovely ta tabbatarda tunaninmu na cewa Israila batada manufar bawa Falasdinawa kasarsu ta Kansu, wannan ya tabbatar man da cewa an fara kenan kuma babu makawa wannan badakalar yaki ne kawai zai kawo karshenta. 

Tabbas harinda Hamas suka kaiwa kasar Israila a 7 ga watan oktoba abun ayi Allah wadai dashine, wanda ni kaina nayi Allah wadai dashi. 

 Amma irin rashin imani da kisan kiyashi da kake a Gaza yasa shi ya koma kamar wasar yara. 

Tabbas Israila nada yancin kare kanta amma batada yancin yin kisan kiyashi ga mata da kananan yara. 

Tabbas irin rashin imani da kisan kiyashi da kuka nuna yafi muni akan abunda Hamas sukayi. 

Sannan kuma yanzu abunma ya kara muni, saboda irin rashin imani da kuka nuna yasa kungiyar Hamas na kara samun karbuwa a duk fadin duniya. 

Daga bisani, rashin tunaninka, dakikancinka da kuma muguwar aniyarka yasa Hamas ta zamo abar kauna a idon duniya. 


Yanzu a haka sojojin Hamas a karkashin kungiyar Al Qassam Brigade sun kara samun karbuwa a kasashen musulmi na duniya sun zamo abun yabo saboda jaruntarda suka nuna wajen yakar gwamnatin zalunci, share waje zauna da kuma mulkin mallaka na shekaru 75.  

Abunda ya faru a ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 ya fito da lagon Israila, ya kuma nuna cewa zancenda ake na cewa babu sijoji kaman sojin Israila wata zuke ta malle ne kawai, koda kuwa yau Israila ta samu damar kashe duk wani mai numfashi a zirin Gaza, koda kuwa ta rushe duk wani gida a wajen tareda hallaka duk wani abu mai rai. Hamas ta nuna was duniya cewa za,a iya yakar Israila sun kuma shuga irin yakar Israila a zuciyar duk wani balarabe da Muslimi a fadin duniya kuma zasu ci gaba da wannan yakin har abada. 

A kasashe turai d turawan yamma na ganin cewa Hamas kungiyace ta yan ta,adda amma mafiyawancin larabawa da musulman duniya a yanzu sun dauki Hamas a matsayin baradanda suka tashi suka kare Kansu daga zakunci da mulkin mallaka. 

Suna kallon Hamas kamar yadda mafiyawancin bakake yan kasar Afrika ta kudu suka rings kallon jam,iyyar ANC da lokacin yakar wariyar launin fata da ya addabi kasar shekarunda suka gabata. 

Suna kallonsu kamar yadda duniya ta dauki kasashen Ingila, Amurka, Rasha, Belgium, Kanada, Holland da sauran kasashen suka dage damtse suka yaki gamayar kasashen da kasar Jamus ta jagoranta a yakin duniya da biyu. 

Tunanin cewa zaka iya yakar akida ka karfin tuwo ka kuma kashe duk wani mai wannan tunanin to shirmene, haukane kuma batan basira ne da kasar Israila ta shafe shekaru 75 a kai ba tareda nasara ba. 

Tabbas babu shakka wannan kuskuren zai tambayeka kai da kasar ka nan ba da dadewa ba. 

Ina mai adduar cewa Allah ubangiji, mai yau da kullum, mai can can da da yanzu ya taba zuciyarka ya kawo sauyi a tunaninka kafin lokacin ya kure. 

Salam. 

(FFK)









Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post