Dr. Mrs. Mary Alile shugabar matan jam,iyyar APC ta mika sakon fatan alkhairi ga yan takarkaru 34 na jam,iyyar a zaben maye gurbi da zai gudana a ranar Asabar 3/ Febrairu 2024.
A wani sako na musamman shugabar matan tana mai cewa " wannan wata dama ce da zamu sake nunawa duniya irin karbuwa da kuma soyayyar dake tsakanin yan kasa da kuma jam,iyyar tamu ta APC."
Dr. Mrs. Mary ta sake yin kira ga yan takarar dasu yi koyi da irin kyawawan dabi,un jam,iyyar su kuma zamo jakadu na gari a wannan zaben mai zuwa ta hanyar bin doka da tsari da kuma aiki da kaidojin jam,iyyar.
A daidai wannan lokaci da ake kan shirye shirye da gyare gyare tsundumawa wannan zaben Dr. Mary ta yi kira da kuma fatan nasara ga jam,iyyar ta kuma yi kira ga yan jamiyyar maza da mata da su hada karfi da karfe domin cimma nasara.
Dr. Mary ta sake kira ga yan takarar dasu zamnato masu gaskiya, rikon amana da kuma bin doka da oda.
📷 *CAPACITY MEDIA HAUSA*