Hadakar Kungiyoyin Matan APC sun Ziyarci Ofishin Dr. Mrs. Mary Alile

Hadakar kungiyoyin matan jam,iyyar APC masu rejista da ofishin na shugabar matan jam,iyyar sun kai ziyara ta musamman zuwa ofishin shugabar matan a babbar Hedikwatar jam,iyyar dake birnin tarayya Abuja. 

Kungiyar ta kuma bada kyauta ta musamman ga shugabar matan da zimmar tayata murnar zagayowar ranar haihuwarta da akayi a ranar litinin data gabata. 

Wannan gagarumin bikin daya gabata a gidan shugabar matan ya samu halattar masu ruwa da tsaki daga sassa dabban dabban na kasar nan da suka hada da shuwagabanni jam,iyyar, shuwagabanni gwamnati dama shuwagabannin al,umma daga sassa dabban dabban na kasa. 

Dr. Mary ta mika dubun godiya ga wudanda suka tayata murna a wannan muhimmiyar rana ta kuma yi alkawalin ci gaba da dage damtse domin sauke nauyin al,umma da Allah ya dora mata.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post