APC Bata Fitarda Tsarin Zaben Fidda Gwani ba a Jahar Edo

A wata sanarwa ta musamman da ofishin shugabar mata ta jam,iyyar APC Dr. Mrs. Mary Alile ta fitar jam,iyyar tace bata fittada tsarin zaben fidda gwani ba, sabanin jita jitarda ake yadawa a zaben fidda gwanin zaben Gwamnan da za,ayi a wannan shekarar. 

Sanarwa da babban sakataren shugabar matan ya sawa hannu ta jaddada cewa har yanzu jam,iyyar bata cimma matsaya ba akan tsarin zaben fidda gwanin, ta kuma yi kira ga yan jam,iyyar dasu ci gaba da hakuri Jim kadan tsarin zai fito. 

Dr. Mary ta kara kira ga yan jam,iyya dasu ci gaba da bawa jam,iyyar hadinkai tareda da goyon bayan domin cimma manufa da kuma tabbatarda ingantaccen zabenda zai fitarda dan takarar da al,umma zasuyi amanna dashi. 

Daga karshe ta jaddada manufar APC a karkashin jagorance Dr. Abdullahi Umar Ganduje na tabbatarda anyi zabe mai sahihanci an kuma gabatarda dan takara mai inganci dazai ci zabe.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post