Barr. Nana Gani Audu ta Taya Dr. Mrs. Mary Alile Murnar Cika Kwanaki 100 a Ofis

Fatima Musa Sambo

Barr. Gani Audu babbar mai ruwa da tsaki a jam,iyyar APC ta taya shugabar matan jam,iyyar ta kasa Dr. Mrs. Mary Alile murnar cika kwanaki 100 a mukamin nata. Barr. Gani tace Mrs. Mary ta taka rawar gani ta musamman a cikin wudannan kwanaki. 

Barr. Gani ta kara da cewa kokarin Mrs. Mary a cikin wudannan yan kwanakin tabbas abun a yaba ne a kuma yi koyi dashi. 

Ta kara da cewa babu shakka Mrs. Mary ta fuskanci kalubale dabban dabban a wannan matsayin babu kuma wani makasudin tarin nasarorin da Mrs. Mary Alile ta samu a cikin wudannan kwanakin face jajircewarta da kuma sanin makaman aiki. Ta kara da cewa bata da wani shakku akan cancantar Dr. Mary wajen cimma nasara a wannan matsayin da ta samu kanta. 

Barr. Ta kara da taya Dr. Mary murnar wannan mataki da kuma yi mata fatan alkhairi a cikin al,ammurran da suka shafi sauke nauyin al,umma daya rataya a kanta.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post