Zaben Edo: Shugabar Matan Jam,iyyar APC ta Kasa ta Bude Wuta

Ba wata tantama ba kuma wani kuduri bane dake boye akan cewa Dr. Mrs. Mary Alile nada yakikin cewa jam,iyyar APC zata karbi kujerar Gwamnan jahar ta Edo a zabenda za,a gudanar a shekara mai zuwa ta 2024. 

Shugabar matan ta jam, iyyar APC Dr. Mrs. Mary Alile bata yi kasa a guiwa ba wajen dage damtse da shiga da fice domin tabbatarda wannan kudurin. 

Dr. Mrs. Mary Alile tana matukar kokarin ganin an tabbatarda kudurin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen sabunta zato ga yan kasa musamman a jahar ta Edo dake gab da sake zaben Gwamna, tare kuma da tsamo jahar daga halin ni yasu da jahar ta samu kanta sakamakon mulkin shekaru 8 na jam,iyyar PDP wanda ya gurbata cigabanda jahar ta samu a baya. 

Dr. Mary Alile wacce ta fito daga mazabar Evbodobian a karamar hukumar Orhionmwon a jahar ta Edo, nada yakinin cewa jahar ta Edo ta shiga wani mawuyacin hali wanda jahar ta samu kanta a ciki sakamakon mulkin yan wawa na shekaru takwas. A kan wannan maudu,in ne Dr. Mrs. Mary Alile ke kira ga yan Edo maza da mata dasu zabi jam,iyyar ta APC a zaben mai zuwa domin tsamo jahar daga wannan mawuyacin halin.  

Ta kumayi kira ga yan jahar maza da mata dasu guji maimata kuskurenda sukayi a shekarar 2020 na zaben jam,iyyar PDP. 

A matsayinta na shugabar matan jam, iyyar APC Dr. Mrs. Mary Alile ta rantsarda masu taimaka na musamman akan gangamin jama,a guda 18 a ofishinta dake jahar ta Edo a wani yunkuri na tallafawa da kuma hubbasa wajen Janyo hankulan jama,a wajen zaben jam,iyyar ta APC da zimmar cimma nasara a zaben na shekarar 2024. 

Shugabar matan ta jam, iyyar APC ta kasa kuma shugabar kungiyar Sister to Sister tana kira da babbar murya akan a fito a hada karfi da karfe wajen cimma nasara da cikar buri, babu shakka wannan dalilin ne yasa ake mata lakabi da madam "CAPACITY " ko ace cancanta a Hausa.  

 *CAPACITY MEDIA HAUSA*

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post