Dr. Mrs. Mary Alile ta Tura Wakilai a Taron Tallafawa Mata Domin Shiga Harkokin Yau da kullum

A ranar talatan data gabata ne 28 ga watan Nuwamba, 2023, aka gudanarda taron tallafawa  mata akan shiga harkokin yau da kullum da cibiyar kula da tattalin arzikin Najeriya ( Nigeria Economic Summit Group) tare da hadin kan cibiyar kirkire kirkire da kuma tsare tsaren gwamnti (Policy Innovation Centre) tare da hadin kan Majalisar dinkin duniya, Bankin Duniya, Ma,aikatar kasafi da tsare tsare suka gabatar. 

An gudanarda wannan taron ne domin tallafawa mata shiga harkokin yau da kullum a kan mizanin sana,a da kiyon lafiya. 

Babban Darakatan zantarwar taron Dr. Osayi Dirisu a yayinda yake bayanin bude taron yace kudurin taron ya ta,allaka ne akan samo mafita da kuma dabarun yaki da irin tsangwama da akewa mata a wasu sassa na gwamnati,siyasa,kasuwanci da sauran al,amurra na yau da kullum. 

Dr. Dirisu ya nemi a kirkiro wasu dokoki da kuma tsare tsaren gwanati da zasu kare muradin mata su kuma basu damar shiga a dama dasu a kowane sashe na cigaban rayuwa ba tare da tsangwama ko tauye haki ba, musamman a bangaren kiyon lafiya dama kula da lafiyar ita kanta. 

A nata jawabin wakiliyan shugabar matan jam,iyyar ta APC wato kwamaret Victoria Emike Okhai da kuma Hajiya Nana Gani Audu a yayinda suke ganawa da manema labaru sun ce a madadin Dr. Mrs. Mary Alile shugabar kungiyar Sister to Sister Worldwide mai kula da kare hakkin mata ta fahimci bukatar bawa hakkin mata muhimmanci, wannan shine ya kaita da kafa wannan kungiyar. 
Sun kuma kara da cewa shugabar matan ta jam,iyyar APC Dr. Mrs. Mary Alile kullum tana fada cewa kofarta a bude take domin hada karfi da karfe a tallafawa mata. Ta kuma yi alwashin ci gaba da baiwa mata goyon bayan shigowa siyasa domin aji muryarsu kuma a dama dasu. 

Hakama babbar ministan matasa ta kasa wato Dr. Jamila Ibrahim, Dr. Egemba Chinonso ( Akporo Doctor) Dr. Ishak Lawal, da Ugochukwu Nwosu babban Daraktan "End Cervical Nigeria Initiative" kungiya mai yaki da cutar jeji a al,aurar mata dama sauran masu ruwa da tsaki sun tofa albarkacin bakinsu a wannan gagarumin taro.

 *CAPACITY MEDIA HAUSA*

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post