A daidai lokacinda zabe ke kara matsowa haka tsanani ke karuwa sanadiyyar karancin takardun kudi a kasa. Komai ya rikice mutum da kudinsa ya koma almajiri yana rokon a taimaka masa ya samu koda dari Biyar yaci abinci.
A kauyuka da karkara kuwa abunma yafi muni inda talakawa manoma da suka sha bakar wahala wajen noma kayan gonarsu, ga matsalar rashin tsaro ga tsadar rayuwa amma yau dole tasasu suna karya wudannan kayan suna sayarwa a wulakance kawai domin su samu na cefane.
Tabbas ansan musulmi da tawakkali kuma da ace wannan abun yazo bada ganganciba to dole ne a samu ire irenmu da dama wudanda zasu fito su kare muradin gwamnati kaman yadda muka shafe shekaru munayi.
Amma wannan kuncin rayuwar an kirkireshi ne kawai saboda anason a muzgunawa wani mutum daya. Wato saboda mutum dayane aka saka sama da mutane milyan dari da tamanin cikin halin kakanikayi kawai don a hanashi cin zabe.
Idan muka duba kuma mukayi la,akari shin meye laifin wannan bawan Allahn da ake mashi irin wannan makarkashiya da kulla kulla da zimmar a hanashi cin zabe?
Babban laifinshi shine ya taimakawa wannan gwamnatin, a daidai lokacinda kowa ya guji shugaba maici yanzu. A daidai lokacinda Atiku, Kwankwaso, Saraki, Tambuwal da sauran jiga jigan arewa da sukayi kaura daga jam,iyyar PDP suka dawo sabuwar jam,iyyar APC domin kare muradinsu suka kuma hadewa shugaba Buhari kai da zimmar sai sun kadashi a zaben fidda gwani.
A daidai wannan lokacin Ahmed Tinubu ya tsaya tsayin daka da karfinsa, da matsayinsa da dukiyarsa saida ya tabbatar shugaba Buhari da yan anshin shatansa sunyi nasara cikin iyawar Allah.
Haka akazo babban zabe wannan bawan Allah dashi da yan kabilarsa sukayi ruwa sukayi tsaki saida Buhari yaci zabe. Idan bamu manta ba Bubarin nan ya shafe shekaru yana takara amma kuri,unsa na fitowa daga yankin arewa ne kawai saboda haka ya kasa cin zabe.
Amma da taimakon Allah da goyon bayan Tinubu saiga shugaba Buhari yayi nasara.
Ai kyaun dan halak ya maida biki. Nayi tsammanin koda shugaba Buhari bai fito fili ya goyi bayan Tinubu ba kamar yadda Tinubu yayi masa to kada ya fito fili ya nuna kiyayyarsa ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Sai gashi yau saboda Tinubu shugaba Buhari ya zabi ya saka dinbin yan Najeriya cikin kunci da halin kakanikayi wai don ya hana Tinubu cin zabe.
Tun yana boyewa, tun yan kanzaginsa na fitowa suna cewa wai bada saninsa ba ko kuma ace wai wasune ke amfani da wata dama suna abunda sukeso batareda yawunsa ba sai gashi yau ta fito fili har takai ga Shugaba Buhari yayi biris da dokar kotun koli kawai domin ya muzgunawa Tinubu.
Wannan shi ake kira da butulci, cin amana da yaudara. Koda ace shugaba Buhari bai taba yiwa Tinubu alkawalin zai bashi mulkin shugabancin kasar nan ba idan ya gama nashi wa,adin to ai maida biki sai dan halak. Ya kamata ace ya maida biki, ya kamata ace ya nuna halacci.
Duba da hakane na yanke shawarar cewa koda yaya, koda wane hali in sha Allah saina fito na zabi Asiwaju Tinubu kodan mahassada suji kunya.
Da ace shugaba Buhari yayi la,akari da irin tuggu da makircin da aka ringa kulla masa a lokacinda yake neman takara da yagane cewa Allah ke bada mulki ga wanda yaso a lokacinda yaso a idon kowa ko yanaso ko bayaso.
Shugaba Buhari ka bamu kunya kuma zamu zabi Asiwaju Tinubu kodan mahassada suji kunya.
Sunana Mohammed Bello daga Abuja Najeriya.
Tags
Hausa