APC Tayi Alkawalin Yakar Kudurin Canza Kudi, Fito Na Fito Da Buhari.

Manyan masu ruwa da tsaki na jam,iyyar APC sun sha alwashi yakar kudurin gwamnatin tarayya na hana amfani da tsofaffin kudi ba tareda gwamnati ba buga isasshin sababbin kudin ba. Sun kuma sha alwashin yin fito na fito da gwamnatin tarayya akan wannan tsari.

Dan takarar shugaban kasa na jam,iyyar ne ya fara yin wannan kiran a Birnin Ogbomosho ya kuma maimata a Biranen Bauchi da Kebbi. Inda yake cewa wannan tsari tsarine dake saka talakawan kasa cikin kunci da matsala. Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya data kara wa,adi isasshe domin gudun kara tura talakawa cikin halin talauci.  

Haka ma gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir El-rufai da takwaransa na Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje sun fito sun soki wannan lamirin wanda har yakai sun kira taron gwamnonin jam,iyyar inda saga bisani sukaje suka kai korafi a fadar shugaban kasa. 

Bayan kai korafinsu shugaba Buhari ya nemi su bashi kwana bakwai domin ya shawo kan lamarin ya kuma yi tunani kafin ya yanke hukunci. 

Amma ga dukkan alamu gwamnonin basu gamsu da wannan bukata ba Wanda yasa gwamnonin jahohin Kaduna,Zamfara da Kogi suka shigarda fadar shugaban kasa kara a kotun koli inda kotun ta yanke hukuncin tsayarda kudurin gwamnatin tarayyar na hana amfani da tsofaffin kudin. 

Amma da sanyin safiyar yau an samu rahotannin cewa ministan Shari,a Abubakar Malami ya nemi babbar kotun kolin data janye hukuncin. 

Wanda ke nuna alamar cewa gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Buhari batada niyyar kara wani wa,adi na daina karbar tsofaffin kudin dukda cewa babu isasshin sababbin kudin a gari. 

A yayinda yake mayarda martani akan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na daukaka kara Gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello yace mutanenda basa kishin talaka ne kawai zasuyi hamayya da wannan hukunci domin kuwa jama,a na cikin halin ha,ula,i sakamakon wannan tsarin babu kuma abunda ya dace ga duk wata gwamnati data san ciwon kanta da ya wuce ta saukakawa jama,a. 

Kawo yanzu masu ruwa da tsaki na jam,iyyar ta APC da suka fito daga sassa dabban dabban na kasa sun kushe wannan tsari sun kuma sha alwashin yakar wannan muradin. 

Abun mamaki gwamnoni da shuwagabannin jamiyyar PDP da jamiyyun adawa ne kawai ke goyon bayan shugaba Buhari akan wannan lamari. 

Satinda ya gabata dan takarar jam,iyyar na shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya nuna goyon bayansa ga tsarin ya kuma yi kira ga shugaba Buhari da kada ya bada kai bori ya hau.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post