Karancin Man Fetur Da Takardun Kudi Akwai Lauje Cikin Nadi Inji Tinubu.

Yan Najeriya suma daina tantama ko mamakin cewa akwai wasu tsiraru a cikin gwamnatin nan dake hada kai da yan adawa wajen dagulawa da kuma karawa yan kasasa matsatsi domin su cimma wasu bukatu na siyasa.

Da mamaki Asiwaju Bola Tinubu na fitowa ya nuna tausayawa talakawa a halinda suke ciki na matsi saboda rashin man fetur da kuma karancin sababbin kudi sai babbar jamiyyar adawa tayi tsalle ta fadi gefe tana kokarin sauya labarin da zimmar kawo rudani tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da dan takarar na APC senator Tinubu.

Akace mara gaskiya ko cikin ruwa yayi jibi.

Hakikanin abunda ya faru shine Bola Tinubu bai soki lamirin shugaba Buhari ba a Abeokuta lokacinda ya koka akan halin matsatsinda talakawa ke fuskanta a kasa.

Asiwaju na kokarin janyo hankalin gwamnati ne akan irin kulla kullar da ke faruwa tsakanin wasu mutane a cikin gwamnati da kuma yan uwansu a PDP.

Idan bamu manta ba gwamnan babban banki na CBN ya dade yana gayawa yan kasa cewa akwai isassun sababbin kudi da zasu ishi yan kasa amma sai gashi an wayi gari samun wudannan kudin ya zamo masifa ga talaka.

A yau dinnan kwana goma kacal suka rage a daina amfani da tsohon kudi amma bankuna da injinan ATM babu inda zakaje ka samu wannan sabon kudin. Wannan ba masifa bane?

Haka kuma shugaba Tinubu yanada masaniyar yadda shugaba Buhari ya ke kokarin ganin anyi maganin matsalar rashin mai a kasa. Hartakai ga shi shugaban ya nada kwamiti na mutum 14 Wanda yake jagora domin magance wannan matsalar. 

A maysayin Tinubu na dan takara dake kishin al,ummah ya dace da ya fito ya yi kira ga shugaba Buhari domin nusar dashi cewa akwai masu yi masa bita da kulli a cikin gwamnatinsa dama wajenta. 

Sannan kuma dan takarar mu akwai ya maimaita magana ce wadda shi kanshi shugaba Buhari yasha fadar cewa akwai masu yiwa gwamnatinsa bita da kulli a cikin gwamnatin.

Tayaya wannan shawarar zata zamo abun muzgunawa ko kushewa? Saidai ga PDP dayake su basa taba kulla alkhairi saidai akasin sa.

Duba da hakan ne mukace kokarin sauya kiran dan takarar mu ga shugaba Buhari da PDP keyo abun dariya ne kuma abun kunya gunsu idan sun sanshi.

PDP da Atiku subi a hankali kada wajen neman kiba su tono rama. Babu wani yunkuri da zasuyi da zai raba kan Buhari da tsohon abokinsa Tinubu.

Yunkurinsu baizai cimma nasara ba, ba kuma zasu samu wani cigaba na siyasa ba ta hanyar sauya kalaman da Tinubu yayi a Abeokuta.

A Matsayin Tinubu na dan takara mai kishin alumma da gwamnatinsa bazai samu waje ya zauna ba ana yiwa gwamnati bita da kulli baice komai ba. 

Kuma a matsayinsa na shugaban jammiyar APC Tinubu bazai bariba yanaji yana gani a shafawa jammiyarsa bakin jini.

Atiku da yan anshin shatansa kan iya ci gaba da soki burutsu da kuma shure shure da bazai hanasu mutuwa ba. 

Kamar yadda Tinubu ya fada a Abeokuta wannan kulle kullen ba zasu hanashi samun nasara ba 25 ga watan febrairu. Ba kuma zasu hanashi da jammiyar APC maida hankali wajen magance matsalolinda PDP da Atiku suka saka jefa yan Najeriya cikin ba. 

Atiku da yan anshin shatansa zasu iya ci gaba da soki burutsunsu, kulla kulla da kuma soke soke amma yan Najeriya sun gane kunnen jaki ba kashi bane tsokace ba kuma zasu bada kai bori ya hau ba. 

Bayo Onanuga
Babban Darakta yada labarai na kungiyar yakin neman zabe na APC. 
January 26, 2023

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post