.... Ya kuma kirasu jam,iyyar bunkasa talauci.
Dan takarar shugaban kasa na jam,iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya zargi jam,iyyar adawa ta PDP da yin makarkashiyarda ta janyo rashin man fetur a kasa domin su cimma manufafin siyasa.
Yayi wannan jawabin ne a birnin Makurdi jahar Benue inda yake ganawa da dubun dubatar magoya baya a taron kamfe na kasa da jam,iyyar ta gudanar yau a Birnin na Makurdi. Tinubu yace idan ba,a manta ba PDP ce ta baiwa yan jam,iyyarta, magoya bayanta dama yan anshin shatansu lasisin shigowa da kuma sayarda mai Najeriya wudanda a yanzu sune ke boye mai din domin janyowa gwamnati bakin jini suna da bata suna.
Inda ya kira jamiyyar da suna jam,iyyar bunkasawa da habbaka talauci.
Yace sun tarar da farashin danyen mai mai kyau a lokacinda suke mulki amma a tsawon shekaru 16 basu kulla wani Abu kirki ba. Sune wudanda na kira lauje cikin nadi a jiya.
Dan takarar yaci gaba da cewa Atiku baisan ya karya dokar aiki ta kasa ba a lokacinda yake aikin gwamnati kuma ya cuwacuwan motocin sufuri a lokacinda yake ma,aikacin kwastam.
Da yan jarida suka tambayeshi hanyarda yabi ya samu kudinsa sai yace wai daga sana,ar sufuri. Baisan cewa hakan ma laifi bane. Iya sanarda doka ta lamuncewa ma,aikacin gwamnati yayi a lokacinda yake aiki shine noma.
Da yake magana akan matasa Tinubu yayi musu alkawalin ingantaccen ilimi da kuma bawa yan makaranta bashi domin su dauki nayin karatun su da kansu. Ya fadi hakan ne a wani shiryayyen jawabi daya zo dashi filin taron.
Ya kuma yi alkawalin maimaita irin nasarorinda gwamnatinsa ta samu a lokacinda yake gwamna a Lagos. Inda yace wudannan nasarorin sune suka sa dan takarar jam,iyyar Labor yayi hijira daga jaharsa ta anambra zuwa Lagos domin cin moriyar Nasarorinda Tinubu ya samu a gwamnati.
A harkar noma Tinubu yayi alkawalin idan aka zabeshi zai kirkiri cibiyoyin noma da zasu taimakawa manoma domin su habbaka kasuwancinsu na noma.
Ya kuma yi alkawalin mayarda jahar Benue ta zamo shugaba akan harkar noma domin habbaka tattalin arzikin jahar.
Ba wai noma kawai zamu maida hankali akai ba, gwamnati zata koyawa manoma fasaha ta zamani domin gyara kayak noma ta kuma daga darajarsa domin sayarwa ciki da wajen kasa da kuma Karin riba.
" Gwamnati na zata kafa cibiyar kula ta kudaden kayan gona domin cimma wata matsaya akan farashin muhimman kayan abinci. Zamu kuma kirkiri gundumomi na noma domin bama manoma damar samun rancen kudin noma da kayan aiki cikin sauki. Domin yin amfani da fasahohi na zamani wajen bunkasa ayukan noma.
Haka kuma a kan ma,adinai gwamnati zata bada himma kwallin kura, kuza, tin da sauran ma,adinai domin a tono su akuma sayar dasu ciki da wajen kasa domin amfanin dan Najeriya.
Akan harkar tsaro kuwa Tinubu yana cewa " Gwamnatina zata saka hannun jari akan harkokin demokradiyya masu nagarta da zasu inganta tsaro. Munji kukanku akan rashin tsaro kuma munyi alkawalin zamu share maku hawaye.
" Shirye shiryen mu a bangaren tsaro zamuyi aiki tukuru wajen kare jinin bil adama da kuma kare filayensa da gonaki. Zamu mayarda hankali sosai wajen kula da tsaro domin magance ta,addanci, banbadanci da kuma fashi da makami.
Da yake jawabi a taron ministan harkoki na musamman kuma tsohon gwamnan jahar ta Benue Senator George Akume ya yaba kwazo da basira da kuma iya mulkin dan takarar na APC. Ya kuma yi kira ga mutanen jahar Benue dasu fito kwansu da kwarkwata ranar 25 ga watan February domin su kadawa Tinubu da sauran yan takarar jam,iyyar APC kuria.
Ministan ya tabbatarwa yan jamiyya cewa yasan Senator Tinubu tun shekarar 1993 ya kuma tabbatar masu da cewa Tinubu abokin jamaar Benue ne zasu kuma iya aminta dashi.
Ya kuma tabbatar masu da cewa Tinubu da mataimakinsa Senator Shetima mutane ne marasa kabilanci da rashin nuna banbancin addini. Ya kara da tuna masu cewa Shetima yayi kokari wajen sake ginawa kiristocin Borno wajajen bautarsu da yan Book Haram suka kona.
Hakama babban daraktan yakin neman zabe na APC kuma gwamnan jahar plateau Simon Lalong, Mataimakin shugaban jamiyyar APC ta kasa Arewa maso gabas Senator Abubakar Kyari, da kuma dan takarar gwamna na jahar Benue Reverend Hyacinth Alia duk sunyi shaida mai kyau dangane da Tinubu sun kuma yi kira ga jama,ar Benue dasu fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi Tinubu.
Manyan bakinda suka samu halattar taron sun hada da Senator Kashim Shetima, gwamnan Niger Abubakar Sani Bello, tsohon gwamnan jahar Edo Com. Adams Oshiomole, Senator Barnabas Gemade da sauransu.
Ofishin yada labarai na Tinubu.
Abdulaziz Abdulaziz
January 26, 2023.
Tags
Hausa