Tauraruwa Hafsat Saed Tace Kano ta G3 ce wato Ganduje, Gawuna, Garo.

Tauraruwa masana,antar Kannywood kuma yar Siyasa National Coordinator ta kungiyar Northern accountability Project support Tinubu tace 2023 idan sunanka bai fara da Kalmar G ba ka manta da cin zaben 2023.

Akan zancen yan kwankwasiyya kuwa tace a gayawa Kwankwasiyya cewa Kanawa sun gane kunnen jaki ba kashi bane tsokace don haka bazasu bar jaki ba suje suna dukan taiki.

Matashiyar wadda kuma member ce ta presidential campaign council na APC tace haka ma Tinubu zai buga Atiku da kasa saboda yan Najeriya cancanta da kuma dacewa suke bukata bawai kabilanci da bangaranci ba. 

Tace Tinubu ya nunawa yan arewa kauna " ku dubafa Ku gani so nawa Tinubu yana goyon bayan yan arewa a lokuta mabanbanta. 

Ya bawa Atiku Abubakar tikitin takara, ya bawa Nuhu Ribadu haka kuma ya goyi bayan Buhari har yaci zabe, shin su masu ikirarin taimakon arewar wasuka taimakawa a arewan? Babu dagasu sai yayansu.

Don haka arewa ba butulu bace in sha Allah zaben shekara mai zuwa zabe ne na maida biki. Inji sakkwatawa sukace za,a maida wa kura aniyarta


Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post