Shugaban Kungiyar nan ta farko a jahar Kano dama Najeriya gaba daya mai goyon bayan dan takarar shugaban kasar Najeriya a Jam,iyyar APC wato Tinubu Media Team Comrade Nura Ahmed Bichi yace ruwa ba tsaran kwando bane.
Ya tabbatarwa Jami,an ANN a wata hira ta mussan da yayi dasu ta wayar tafi da gidanka cewa APC zata lashe zaben 2023 da karfin Allah.
Da aka tambayeshi ya baya ganin cewa tsohon gwamnan Kano wato sanata Rabi,u Musa Kwankwaso zai iya zama barazana ga jam,iyyar tasu ta APC comrade Nura yana cewa " Tabbas Mai girma Sanata Kwankwaso ba karamin dan siyasa bane amma ina mai tabbatar maka ruwa ba tsaran kwando bane Mai girma gwamna ya wuce inda suke tsammani. Yasha alwashin cewa Ganduje zai yiwa Kwankwaso bugun gyadar Mahaukaciya.
Da aka tambayeshi akan tsohon shugaban kasa kuwa Comrade Nura yace haba wannan ai kafin Karfe biyu na rana in sha Allahu mun hada mashi jini da majina.
Masana dai naci gaba da kallon siyasar ta jahar Kano inda ake sa tsammanin cewa dole za,ayi kare jini biri jini saboda muhimmacin jahar a siyasar Najeriya.
Tags
Hausa