Fatima Sambo Tace El- Rufai Ba Tsaran Isah Ashiru Bane, Masu Gidansa Ma Sun Fece.


Matashiyar Yar siyasa kuma yar kasuwa shugabar Kamfanin MG-Sambo Collections Fatima M. Sambo tace babu shakka Senator Uba Sani ne Zai lashe zaben gwamnan Kaduna da za,ayi shekara mai zuwa.

Matashiyar wadda kuma member ce ta state campaign council na APC tace yan Kaduna ba mahaukata bane bazasu saki reshe su kama ganye ba. Tana mai cewa aikin da el-rufai yayi wa Kaduna a cikin shekaru bakwai PDP bata yishi ba a cikin shekaru goma sha shida datayi tana mulki.

Ta kara da cewa yan Kaduna na alfari da mai girma gwamna kuma duk inda yasa kafa nan zasu saka suma.

Da muka tambayeta bata ganin akwai kalubale saboda irin yadda gwamnan ya ringa korar maaikata da kuma takaddama tsakaninsa da maaikatan kwadago a jahar tace,

" Jahar Kaduna tafi kowace jaha masu ilimi a arewacin Najeriya don haka munsan muhimmancin ilimi, don Allah taya za,ace malami ya kasa cin jarabawarda ya rubutawa yaranda yake koyarwa sannan kuma a barshi ya ci gaba da koyarwa? Ai kaga an tauye hakin yaran da yake koyarwa kuma an saka jahar a wata turba ta ci baya kenan. Tabbas abun ba dadi amma dole ayi abunda ya dace domin ci gaban kasa da al,umma".

Da aka tambayeta bata ganin cewa Atiku Zai iya kawowa jam,iyyar tasu ta APC barazan tayi murnushi tace "manta da Atiku wannan ai bazawarar mu" mun saba kada ita. In sha Allah Atiku saiya riga rana faduwa. Atiku kamata yayi ya shafe sauran shekarunda yayi a duniya yana neman gafarar yan Najeriya ba wai ya fito ya sake neman mulki a kasar ba.

Tayi kira ga yan Nigeria musamman yan arewa dasuyi amfani da cancanta wajen zaben shuwagabanni ba wai kabilanci ko bangaranci ba. A nata cewar al,adar yan arewa itace musulunci bawai kabilanci ba, kuma duka su biyu din musulmai ne don haka sai ayi aiki da cancanta a bar zancen kabilanci da bangaranci wudanda Sam basa cikin koyarwa addinan musulunci dama kiristanci.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post