Dr Kabiru Shehu Shinkafi tsohon Comptroller na immigration yace baza,a samu zaman lafiya mai dorewa a Zamfara ba sai an samu talakawa sun goyawa gwamnati baya sai kuma gwamnati ta rufawa masu taimaka mata da bayanan sirri asiri.
A wata hira da yayi da Jami, an ANN a babban filin jirgin Sama dake Lagos Dr. Shinkafi yace gwamnati kadai bazata iya inganta tsaro ba ba tare da goyon bayan talakawa ba, haka kuma yan ta,adda bazasu iya cin nasara a kan al,umma ba tare da samun bayanan sirri saga talakawa ba.
Don haka yace yana mai bada shawara ga gwamnati data kawo wani sabon tsarin tattara bayanan sirri domin amfani dasu wajen yakar ta,addanci a Zamfara.
Yana cewa " Yanada muhimmaci idan gwamnati zata kawo wani sabon tsari Wanda yan kasa zasu ringa bada jawaban sirri ga gwamnati, bawai ga yan sanda ko sojoji kadai ba a,a harma da shuwagabannin addini dana siyasa. Sannan kuma a tabbatarda wannan tsari nada kyauta ta musamman ga duk Wanda ya kawo bayaninda har aka samu nasarar koda kama barawo guda ne, a kuma yi adalci a rufawa masu bada bayanan sirri asiri a kuma karesu idan bukatar yin hakan ta taso.
Da aka tambayeshi cewa shin baya ganin akwai sakacin gwamnati wajen ko in kula da shaanin tsaro saboda abun basu yafi shafa ba? Dr Kabiru yace "Wallahi ina tausayawa Gwamna Matawalle, a matsayina na tsohon Jami,in tsaro dayakai har matakin comptroller to inada hanyoyin tattara bayanai na sirri kuma nasa gwamnati na iya kokarinta. Kada fa ka manta dan uwa ne zaije wajen barayi ya gaya masu cewa dan uwansa nada kudi azo a sace shi kawai saboda hassada, ganin gyashi da son duniya. Wallahi abun ya wuce duk inda kake tsammani.
Dangane da siyasar 2023 kuma Dr Kabiru yayi wa Zamfarawa albishir na cewa tabbas idan Sanata Tinubu ya lashe zaben zaiyi abubuwanda suka dace wajen tabbatarda tsaro saboda yanada kwarewa da cancanta wajen tafiyarda mulkin demokradiyya.