Gwamnan jahar Plateau ya tabka wani mummunan kuskure inda ya karbi bakuncin jakadan kasar Israila a Najeriya. Mutumenda yayi kaurin suna wajen ta,addanci, kisan kiyashi , leken asiri, da kisan kare dangi. Na kalli wannan video kamar inyi haraswa.
A matsayin Muftwang na kirista shin ya yakeji idan yana cudanya da yan ta,adda, azzalumai, ma yaudara masu kisan kiyashi da kisan kare dangi?
Abu mafi muhimmanci ma shine a matsayinsa na da Adam yayake iya bacci da dare bayan yin hakan kuma yana sane?
Baya ga haka shin yanada masaniya akan irin rawarda kasar Israila ke takawa wajen ci gaba da irin wannan kisan kiyashi da zubarda jini da ke gudana a Arewacin Najeriya. Dama jaharsa ta Plateau?
Shin yanada masaniya akan su waye ke daukar nauyin wudannan kashe kashen da ke gudana a Najeriya kudu da Arewa?
Shin yasan su waye ke cin moriyar wannan zubarda jini da akeyi?
Shin yasan da cewa bukatarsu shine su janyo yakin basasa a Najeriya su fake da hakan su wawashe dukiyarmu?
Ya kamata a gaya mashi ya tambayi iyayen gidanshi zayonawa wudanda suka kirkiri kungiyoyin Boko Haram, ISIS,ISWAP, ALQAIDA dama duk wata kungiyar ta, addanci a fadin duniya.
A gaya mashi ya tambayesu shin wake amfani da irin wudannan kungiyoyin wajen tarwatsa kasashe da Kuma mamaye su.
A gaya mashi ya tambayesu shin meyasa duk cikin wudannan kungiyoyin babu wata kungiyarda ta taba kaiwa Israila hari?
A gaya mashi ya tambayesu shin wace kasa ce tafi dagewa wajen sayarwa sojojin Biyafara makamai a lokacin yakin basasar kasar nan?
A gaya mashi ya tambayesu shin wace irin tarba suka yiwa Yahudawan Ethiopia bakaken fata yayinda suka nemi zama yan kasar Israila. Inda aka ringa yi masu allurar hana haihuwa domin a hanasu yaduwa a cikin kasar.
Tabbas karbar da Muftwang yayiwa jakadan azzalumar kasa, kasar yan share wuri zauna, yan ta,adda ba karamin rashin adalci bane da kuma yin ko in kula da mummunan rashin imaninda wannan dan ta,addan Benjamin Natenyaho ke yiwa mata da kananan yara a zirin Gaza dama kasar Palestine baki daya.
Baya ga haka Gwamna Muftwang yayiwa jaharsa mummunar illa a addinance da al,adance.
Yin sumogal din Bayahude ka shigarda shi gidanka bazai taba taimaka maka ba wajen magance matsalolinda kake fuskanta ba saidai ma ya Kara maka wasu.
Kamar yadda ake cewa kula da Girkawa (Greeks ) harma dai idan sunzo maka da kyauta. Tabbas al,ummar Troy sun koyi wannan darasin ta hanya mai wahala.
Koda yake shin bakon naka ya gayama irin yadda suka tsani kirista a kasarsu war suke tofa masu yawu?
Shin sun gaya maka cewa kamar yadda yake rubuce a littafinsu na Talmud cewa abun bautar kirista Yesu Almasihu makaryaci ne dan ta,adda wanda yanzu a haka yana konewa a jahannama?
Shin ya gaya maka cewa kamar yadda suka tsani musulmi haka suka tsani kirista kuma haka suke azabtarda su a gidajen yari?
Naji ance washe gari bayan ya bar jahar Plateau yan ta adda suka kashe sama da mutum 100 a jahar. Banyi mamakin hakan ba domin kuwa ai abun a bayyane yake.
Tabbas Muftwang na bukatar darussa da yawa
Femi Fani Kayode Sadaukin Shinkafi, Wakilin Doka Potiskum, Otunba Joga Oriole. Kuma tsohon ministan al,adu da yawon buda ido kuma tsohon Ministan sufurin Jiragen sama a Najeriya sannan tsohon babban mai bada shawara ga tsohon sugaban kasa Obasanjo.
Tags
News