Shugaban kasa Trump, a cikin watanni 15 da suka gabata, ƙasarku Amurka dage damtse wajen jefa mutanen Gaza cikin wani mummunan hali daya kunshi kisan gilla, kisan kare dangi, da kuma yunkurin share su daga doron ƙasa.
Kun ba da makamai, tallafin kudi, da duk wani taimako da ya ba da dama ga Isra’ila ta aiwatarda wannan mummunar ta,asa, bisa amincewarku an gallazawa dubban daruruwan fararen hula da basuji ba basu gani ba a zirin Gaza, mafi yawansu mata da kananan yara ne.
Kun mai da kyakkyawar ƙasarsu da ta kasance gwanin shaawa a baya ta zamo gurɓatacciya, cike da guba, Kun yiwa mata da kananan yara gunduwa-gunduwa, Kun mayarda Gaza kufai cike da gawawwaki masu wari da kwari ke ci.
Kun aikata wannan ta hanyar ba wa Isra’ila mafi munin makaman zamani, ciki har da bama-bamai da nauyinsu ya zarce tan 2000, waɗanda suka zuba kan talakawan Gaza marasa ƙarfi, matalauta, kuma marasa kariya. Wannan ba komai ba ne illa kisan gilla da ba a taɓa ganin irinsa a tarihin ba.
Kun ragargaza su a jiki, a ruhi, da kuma a zuciya.
Amma har yanzu ƙasarku ba ta ƙoshi ba. Da zaran kun hau mulki, abin da ya firgita duniya gaba ɗaya shi ne, kun bayyana muguwar manufarku ta kwace Gaza, inda har yanzu akwai mutane 1.6 miliyan da suka rage a raye (wudanda a baya sun kai miliyan misalin milyan biyu da rabi), domin ku mayar da ƙasarsu wani kyakkyawan waje don kasuwanci da yawon buɗe ido na attajiran Amurka!( Kamar yadda kuka fada)
Duk da cewa ƙasace da mutanen Falasdinu suka zauna fiye da shekaru 2000 da suka gabata.
Wannan ita ce ƙasar da abokanku 'yan zahyoniyya masu kishin zubarda jini suka kasance suna kashe Wanda suka so, suna azabtarda ilahirin al,ummarta ta hanyar horo da yunwa, talauchi da kuntata masu tsawon shekaru 76.
Wannan ita ce ƙasar da miliyoyin mutanensu suka gwabza jihadi tareda sadaukarda jininsu da rayuwarsu tsawon shekaru saba’in domin kare mutuncinsu, darajarsu, tarihi da asalin su, da zimmar barin tarihi ga zuriyarsu masu zuwa.
Kun kai ga cewa kuna da "niyyar mallakar Gaza" kuma kuna fatan " wasu ƙasashe su inganta wasu sassa na Gaza domin ya zama kyakkyawan wuri da mutane daga wasu sassa na duniya zasu iya zuwa su zauna.”
A ƙarshe, kun ce “’yan asalin Falasdinu ba za su sami haƙƙin dawowa ba idan sun tafi.”
Kamar yadda Jakadan Israila a Indiya Mr. A. M. Shawesh yake cewa.
"Duk Lokacin da dan fasa kwaurin filaye ya zama shugaba a duniya, to ba wanda zai tsira, dole kowa yayi biyayya."
Babu shakka Rashin tausayi da kuka nuna ga mata da yara na Gaza abin Allah wadai ne.
Saboda baku iya jin radadin da suke ciki da gazawarku wajen fahimtar hawayensu yana nuna cewa ba ku da imani ko tausayin dan Adam.
Ba kawai kuna so ku kwace abin da ya rage a hannunsu ba, har ma kuna son kwashe Falasdinawa 1.6 miliyan da suka rage su koma Masar da Jordan (wadanda duka sun ƙi amincewa da wannan shiri) sannan ku mai da ƙasarsu wajen shakatawa cike da otal-otal na Amurka, gidajen shakatawar mata masu sayar da jikinsu, da gidajen caca.
Wannan shine ra’ayin mafi yawancin ƙasashen duniya ciki har da Ireland, Afirka ta Kudu, Brazil, Sin, Rasha, Iran, da Sfaniya waɗanda suka jagoranci wannan gwagwarmaya.
Ba Musulmi da Larabawa kawai ke da wannan ra'ayi ba: Babban Limamin Cocin Katolika, Pope Francis, da mafi yawan Kiristoci a duniya suna tare da wannan ra,ayi.
Kashe mata da yara da basuji ba basu gani ba, jefa su cikin kisan gilla, share su daga doron ƙasa, da tilasta musu barin ƙasarsu domin karɓar ta da ƙarfi ba za a iya halatta shi a kowane hali ba.
Shin wannan abu ne mai wahalar fahimta?
Za ku tuna cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana matsayin mutanen Najeriya da kyau lokacin da ya ce a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya:
“A yau muna shaidar matsananciyar wahalarwa da ake bawa mutanen Gaza da sauran yankunan Falasdinu. Ramuwar gayya bazata taba zama adalci ba. ‘Yanci wani haƙƙi ne na dabi’a da ba za a iya hana wata al’umma ba. Mutanen Falasdinu sun cancanci ‘yancin kansu. Sun cancanci samun ƙasa tasu a yankunan da wannan Majalisa da dokokin duniya suka amince da su, waɗanda ake ta yin watsi da su.”
Maganarsa na wakiltar matsayi kasashe 149 da suka amince da Falasdinu a matsayin ƙasa mai ‘yancin kai da cikakken iko.
Ina alfahari da cewa ƙasata ta ɗauki irin wannan matsayi mai daraja, kuma, sabanin taku matsayar, ta zaɓi tsayawa tsayin daka don tabbatarda zaman lafiya da adalci a doron kasa.
Na daɗe ina girmama ku saboda abin da na ɗauka a matsayin tsoron Allah da kuke da shi, ƙimomin addinin Kirista, da niyyarku ta janye Amurka daga yaƙe-yaƙen ƙetare, kusancinku da Rasha, Sin, da Koriya ta Arewa, adawarku da masu fafutukar mulkin duniya, da goyon bayan ku ga masu kishin ƙasa.
Haka kuma, na daɗe ina mutunta ku saboda yadda kuka tsaya da sau da kafa wajen fuskar tsanantawa da azaba da kuka fuskanta daga 'Deep State'.
Duk da wannan mutuntawa, dole ne in gaya muku gaskiya.
Ba lokaci bane na cacar baki da gardama ko furta kalmomin wawanci daga mai bauta wa azzalumai ba ne.
Dole ne in yi magana a sarari.
Zan fara da cewa shirin da kuka yi wa Gaza wata manufa ce ta zalunci da cin amana maras misali.
Yayin da wasu ke maganar kafa tsarin ‘kasa biyu’ da zai ba wa Falasdinawa da Isra’ilawa damar rayuwa tare cikin aminci da zaman lafiya, ku kuwa kuna maganar mallake Gaza da kuma karɓar rijiyoyin man fetur da iskar gas na yankin da karfin tuwo.
Shin babu iyaka ga kwaɗayin kune? Shin wannan matuƙar sha’awa da kuke da ita ta wawure dukiyar wasu, kwace ƙasarsu, da shafe su daga doron ƙasa domin kawai ku mallaki arzikin ƙasarsu, ba alamar shaidanci ba ce?
Shin ba wannan ne abin da fararen fata na Amurka suka yi wa ‘yan asalin ƙasar Amurka (‘Red Indians’) ba?
Shin ba wannan ne abin da Fir’auna, Genghis Khan, Atila, Hun, Christopher Columbus, da Adolf Hitler suka yi wa wasu a zamaninsu ba?
Shin ba su kawar da mutanensu ba, sun kore su daga doron ƙasa, sun ƙone su, sun halaka su, sannan suka karɓi ƙasashensu ba?
Shin wannan ba irin tashin hankali, kisan gilla, yaki, cin zalin marasa ƙarfi, da wawure arziki ba ne ?
Sai kuma ku zo da kalamai na wawanci da barazanar banza irin ta yan fashi, azzalumai mahandama.
Misali, lokacin da kuka cewa "duk wani bala'i zai iya aukuwa idan Hamas ba ta saki duk sauran fursunonin da take rike da su nan da ranar Asabar ba," kun nuna jahilcin ku na cewa Hamas ta fi ƙarfi a yau fiye da yadda take kafin ranar 7 ga Oktoba .
Wannan kuwa ya faru ne sakamakon yawan mata da yara na Falasdinu da kuka taimakawa Isra’ila ta kashe bayan 7 ga Oktoba da sunan ramuwar gayya.
Hamas sun ƙara ƙarfi tareda samun sababbin sojoj saboda burinsu na ramuwar gayya, idan a da suna da mayaƙa 10,000 kafin 7 ga Oktoba, yanzu suna da akalla 200,000.
Iya yawan .Falasdinawanda basuji basu gani ba da kuka kashe, haka Hamas za ta ci gaba da ƙara ƙarfi.
Wannan shine dalilin da yasa ake kwatanta Gaza da "makabartar yan mulkin mallaka."
Abu mafi muni, "wutar da kuke barazanar kunna wa na iya ƙone Isra’ila da kuma yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya.
Tabbas, yin ƙoƙari wajen tabbatar da cewa ba a karya yarjejeniyar tsagaita wuta ba, da kuma ci gaba da tattaunawa don sakin fursunoni daga duka ɓangarorin, yafi alheri fiye da yin barazanar da ka iya jefa rayuwar fursunonin da kuke ƙoƙarin cetowa cikin haɗari.
Ina fatan za ku samu hikimar fahimtar wannan batu.
Shagaltar kanku da tsoma baki a harkokin sauran ƙasashe da kuma da’awar mallakar yankunansu—ko Kanada, Grinlan, Mashigar Panama, Tekun Mexico, Afirka ta Kudu, Colombia ko Gaza— alama ce ta zuciya mai kwadayi da ta kasance mabudin wahala.
Ku kenan Idan ba kuna barazanar kwatar wasu ƙasashe ba, to kuna barazanar janye taimako ko kuma sanya wa cinikayyar su haraji domin durƙusar da su.
Mafi muni kuwa shine ƙyamar da kuke yi wa ‘yan gudun hijira da kuma shirin mayar da su ƙasashensu cikin sarƙa ba tare da wani jinƙai ko mutuntawa ba, ko kuma kulle su a gidan yarin Guantanamo Bay, yayin da a gefe guda kuke bai wa fararen fata ‘yan Afirka ta Kudu matsayi na musamman na ‘yan gudun hijira.
Hakan yana bayyana a fili tsantsar bambancin launin fata da ke zuciyarku.
Rashin amincewarku da ‘yan gudun hijira da kuma kira da kuke yi musu da "masu laifi, ‘yan daba, ‘yan fashi da masu tabin hankali" abin kunya ne.
Bari in tunatar da ku cewa ku jikokin wani ɗan gudun hijira ne daga Jamus, ‘ya’yan wata ‘yar gudun hijira daga Scotland, mijin wata ‘yar gudun hijira daga Slovenia, kuma tsohon mijin wata ‘yar gudun hijira daga Czech Republic.
Kun amfana da manufofin shige da fice na Amurka, amma duk da haka kuna ƙin ‘yan gudun hijira da gagarumar ƙiyayya, tare da ƙoƙarin hana su shigowa ƙasarku, hana ‘yan kasashen waje da aka haifa a can ‘yancin zama ‘yan ƙasa, da kuma soke dokar haihuwa ta ƙasa da ke cikin kundin tsarin mulkinku.
Wannan ƙiyayya ce ga ‘yan gudun hijira wadda har ta kai ga Babban Limamin Cocin Katolika, Pope Francis, ya gaza jurewa har sai da ya fitar da sanarwa domin rage raɗaɗin zafafan kalaman da kuka fitar.
Yana cewa,
"Ina kira ga dukkan mabiya Cocin Katolika da kada su yarda da labaran ƙarya da ake jefawa ‘yan gudun hijira da zimmar jefasu cikin wahala maras tushe.”
"Mayar da Amurka kasaitacciya (Making America Great Again)" ba yana nufin rushe burikan wasu mutane ba, kuma ba ya ba ku haƙƙin yin barazana, danniya da cin zarafin sauran ƙasashe bane!
Ya kamata ku tuna cewa addu’o’in miliyoyin mutane ga Allah ne suka kuɓutar da ku daga harsashin wani mai hari a lokuta biyu mabanbanta, suka hana ku shiga kurkuku, kuma suka kai ku ga matsayin da kuke a yau.
Waɗancan addu’o’in ne za su sa ku durƙushe idan ba ku canza salon tafiya ba.
Allah ya shiryar da ku.
(Chief Femi Fani-Kayode shi ne Sadaukin Shinkafi, Wakilin Doka Potiskum, tsohon Ministan Al’adu da yawon shakatawa, da kuma tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama.)
Tags
Hausa