Kiyayyar Kemi Badenoch Ga Najeriya: Martanin Cif Femi Fani-Kayode Sadaukin Shinkafi

Rubutawa Cif Femi Fani Kayode Sadaukin Shinkafi 

"Abin ban sha’awa ne yadda kowa ke kira na da ‘yar Najeriya. Ni kam na fi danganta kaina da kabilata ta musamman. Ba ni da wata alaka da mutanen arewacin Nijeriya yan Boko Haram, masu tsattsauran ra,ayin addinin Islama . Nafi ganin kaina a matsayin ‘yar bayarrabiya  shi ne asalina, kuma na ki a dunkule ni da mutanen arewa, wadanda muka kasance abokan gaba na kabilanci, kawai don a kira ni ‘yar Najeriya." - @KemiBadenoch.

Kemi Badenoch MP, shugabar jam’iyyar Conservative ta Birtaniya kuma shugabar ‘yan hamayya a Majalisar ta Burtanayi @UKParliament, ba ta tsaya ga zagin kasarmu kawai ba, sai da ta kara da kokarin raba kawunanmu bisa layin kabilanci.

Ta yi ikirarin cewa ba ta taba daukar kanta a matsayin ‘yar Najeriya ba, sai dai Yoruba, kuma ba ta taba ganin wata alaka tsakaninta da mutanen arewacin kasar, wadanda ta kira a matsayin "‘yan Boko Haram da ‘yan ta’adda."

Wudannan maganganu ne masu hatsari daga wata bakar fata ‘yar kasar waje wacce ba ta san komai game da kasarmu ba, ba ta san matsayinta ba, kuma ta nace kan tada rikici wanda ba za ta iya shawo kansa ba, har ma yana iya hallaka ta.

A misali kamar ta ce ta fi ganin kanta a matsayin ‘yar Ingila fiye da ta hada wata alaka da ‘yan Scots da Welsh, wudanda ta dauka a matsayin ‘yan ta,adda mahaukata da suka taba kasancewa abokan yakin kabilancin na Ingilawa!

Duk wannan yana fitowa daga wata matashiya bakar fata, dake jahorancin siyasa a kasa mai kabilu daban-daban, addinai daban-daban, da al’adu daban-daban, wacce ta ke ikirarin cewa ita ce misalin kyawawan dabi’u da al’adu! Wannan babban rudani ne da ba za a iya fahimta ba.

Manufarta ba ta da kyau kuma tana da mugun nufi, tana kokarin raina mu, cin mutuncinmu, da kokarin raba kanmu domin durkusar da mu.

Ina tambaya, me ya faru da wannan halitta tun tana yarinya daya harfarda wannan tsananin kiyayya ga Najeriya?

Ko akwai wani abu da ya faru da ita lokacin da take zaune a nan wanda ta boye?

Ko kuwa ta taba fuskantar wata irin muguwar dabi’a, cin zarafi, ko tauye hakki da ya haifar mata da damuwa, lalacewar tunani mai zurfi, da matsalar tabin hankali?

Shin wannan ne ya sa zuciyarta ke tafasa tana neman fusata duk lokacin da ta ji an ambaci "Najeriya"?

Me yasa jin sunan kasarmu yake janyo irin wannan fusata mai tsanani da rashin kwanciyar hankali a cikin zuciyarta?

Idan aka yi la’akari da irin tsananin kiyayyar da take yi mana, wadannan tambayoyi ne da suka  cancanta da ake bukatar samun amsoshinsu.

Ta tsane mu da irin kiyayyar da Littafi Mai Tsarki ya kira "kiyayya cikakkiya," amma a cikin wata budaddiyar wasika da aka wallafa a kafafen yada labarai  a shekarar 2010, yayin da take neman shiga majalisar wakilan Ingila a karon farko, ta roki al’ummar Najeriya a mazabarta su goyi bayan ta.

A lokacin, tana bukatar mu, ta ga kanta a matsayin ‘yar Najeriya. Amma duk wannan ya sauya bayan da aka zabe ta.

A lokacin, a cikin rudanin tunaninta, duk ‘yan Najeriya sun zama shaidanu, duk ‘yan Ingila sun zama mala’iku, kuma ta fito fili ta bayyana tsananin raini da rashin girmamawar da take yi mana!

Ta tsane mu da tsananin kiyayya amma har yanzu tana da karfin gwiwar dawowa kasarmu tare da wani Hamish, wanda aka ce shi ne mijinta dan Ingila, don kallon wasan polo a Lagos Polo Club.

Wannan Ita Ce Kasa Da Ta Ce Cikin Ta Kamar Daji Ne Mai Cike Da Rashin Doka, Gidan Cin Hanci Da Rashawa, Da Wata Matsatsiyar Gini Mai Tsami Da Ba Zai Haifar Da Alheri Ba, Cike Da Birrai, Dabbobi, Da Mahaukata Marasa Hankali.

Gaskiyar magana ita ce wannan halitta da ake kira Kemi Badenoch ba komai ba ce face wata macijiya mai dafi da ke bukatar a yi mata bulala sannan a kulle ta a keji.

Ita ce Aunty Jemima mai kuzari kamar ta sha kwaya, kuma ita ce shugabar kungiyar duniya ta International House Nigers Association.* Wato shugabar bayi na musamman na kasa da kasa. 

Idan har tana da fasfo na Najeriya har yanzu, ya kamata a kwace shi, kuma kar a sake barin ta taka kasa mai tsarki ta Najeriya da kafarta mai cutar kuturta.

Ya kamata ta dauki shawarar Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima (@KashimSM), da muhimmanci ta cire sunan "Kemi" daga jerin sunayenta.

Ya kamata ta goge sunan aurenta na Adegoke daga kowane rikodi, ta kuma fito fili ta yi watsi da mahaifinta, mahaifiyarta, ‘yan uwanta, da asalinta na Najeriya gaba daya.

Ba ta son a danganta ta da mu, mu ma ba mu son danganta kanmu da ita.

Ta dauke mu a matsayin marasa gaskiya da mugaye, mu kuma muna ganinta a matsayin sheɗan da aka haifa daga Iblis. Babu wata alaka tsakaninmu da ita.

Gaskiya ita ce, ba kawai ta kasance wata matsala ce ta maras muhimmanci ko abin dariya ba, amma yanzu za a iya bayyana ta a matsayin makiyar kasa ta daya ga ƙasar da muke ƙauna.

Ya kamata ta maida hankalinta ga harkokin kasar Burtaniya, ta mayar da hankali kan jam’iyyar mulki ta Labour da Firayim Ministan su Keir Starmer (@Keir_Starmer), sannan ta BARI NAJERIYA TA HUTA!

A bangare mai sauki, abin takaici ne cewa na daina buga wasan polo shekaru da dama da suka wuce. Domin da ace a zamanina ne ta yi kokarin ziyartar Lagos Polo Club, da ba ta wuce kofar shiga ba, kuma idan har ta samu damar shiga, da ‘yan aiki da ma’aikatan dawakai sun chakudata cikin shara, sun dinga yayyafa mata kashin dawakan Argentina, kafin su yagalgalata tareda titsiyeta. 

Tabbas yadda duniya ta sauya kuwa, abin al’ajabi ne!

(FFK)

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post