_To, ga shi, zan sa su waɗanda suke daga jama'ar Shaiɗan, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, ƙarya suke yi, zan sa su, su zo, su kwanta a gabanka, su sani dai na ƙaunace ka. - Ru’ya ta Yahaya : 3 :9-9_
Babu ko shakka wannan ayar daga littafi mai tsarki na magana ne da jabun Yahudawa yan kama wuri zaune da a yau ke zauna a kasar Izraila.
Mafi munin zancen shine a cikin littafin Yahaya 8:44 Yesu Almasihu ya kira su wudannan jabun Yahudawan da sunan yayan Shedan wudanda ke ikirarin cewa su Yahudawa ne amma sam ba Yahudawa bane.
Littafin Nehemiya 23:3-8 ya fayyace mana zancen karara inda yace idan Yesu Almasihu mai ceto ne zai dawo, shi da kanshi zai ja ragamar Yahudawa na gaskiya ya mayardasu kasar Izraila.
Koma dai dame wudannan mutanen sukayi Imani to babu shakka wannan gagarumin al,amarin bai faruba. Sannan kuma kafa kasar Izraila da akayi a shekarar 1948 bashi bane cikar wahayinda littafi mai tsarki yayi ba, ba Kuma wannan bane alkawarin Allah.
Duba da haka da kuma fadar littafi mai tsarki, shin idan wudannan masu ikirarin cewa su Yahudawa ne kuma su ba Yahudawan bane to kenan su suwaye? sannan kuma idan ba saboda Allah aka kafa kasar ba to saboda waye aka kafa wannan kasar, saboda Shedan?
Shin wanene wannan mai cike da alfahari da girman kai da takama da tambarin Annabi Dawuda cike da izgili, girman kai da cin zali, dake kawowa duniya masifa mai dinbin yawa.
Wane bako ne wannan, makaryaci, azzalumi da ke ikirarin farfado da kasar Izraila da zimmar cika alkawurran littafi mai tsarki amma suka zamanto masifa ga makwabtansu, suka kuma kasance musifa ga duniya?
Wudannan tambayoyine da zamu ansa su wani lokaci amma abunda ke gabanmu a yau shine.
Duba da irin dokokin kabilanci da wariyar launin fata a kasar Izraila, da kuma irin kisan kare dangi da ake yiwa mata da kananan Yara a zirin Gaza, Yammacin kogin Jordan dama kasar Lebanon tsawon shekaru 76 da suka gabata babu shakka wannan kasar ta Izraila a yau ta kasance wata kasa azzaluma, kasar wariyar launin fata, masu kisan kiyashi da kuma handama da babakere da batada wani yancin ci gaba da wanzuwa.
Ta kasance wata cibiyar masu tsattsauran ra,ayin addini, abun ki, cibiyar zalunci da yada mummunar manufar yahudu da yahudanci.
Ta kasance wata shedaniyar kasa wacce iya muradinta shine ta shafe duk wani balarabe mace, namiji, karamin yaro ko tsoho da zimmar mamaye kasashen su dake tsakanin Masar, Izuwa Iran.
Idan har kasar Jamus a lokacin Nazi ta rasa yancin ci gaba da wanzuwa sakamakon kisan kiyashi da sukayiwa Yahudawan wancan lokacin yakin duniya na 2 me zai hana kasar Izraila a yau ta rasa wannan yancin akan kisan kiyashi da suka shafe shekaru 80 suna yiwa Falasdinawa?
Ga masu musanta cewa kasar Izraila kasace ta mulkin mallaka da wariyar launin fata ina mai kiransu dasu sake saurarar kalaman Gideon Levi da kunnen basira, Gideon Levi shahararren dan jaridar kasar ta Izraila a wani jawabinda yayi a taron Oxford shekaru kadan da suka gabata inda yake cewa.
" Ni dan kasar Izraila ne, an haifeni a kasar ta Izraila, kuma inason kasata, ina kuma tsananin kishin kasar Izraila, amma babu wani misali anan, karma wani ya kawo zancen hayaniya ko yamutsi ( tsakanin Izraila da Falasdin). A tawa fahimtar babu wata hayaniya ko tashin hankali ( tsakanin Izraila da Falasdin) shin hayaniya akayi tsakanin Faransa da Aljeriya? Babu hayaniya, mulkin mallaka ne da Faransa tayiwa Aljeriya kuma aka kai karshenshi, akaga bayansa, haka zalika babu wata hayaniya tsakanin Izraila da Falasdin, mummunan mulkin mallaka ne da wariyar launin fata wanda shima dole wata rana yazo karshe. A bayan gidajenmu akwai wata gwamnati wadda ta kasance azzaluma, macuciya, mayaudariya ta gani da fada a doron duniya. Nasan me nake fada saboda na kasance Ina daukar rahotanni a wannan kasar harna tsawon shekaru 40, babu wani suna daya dace da wannan gwamnatin face mulkin mallaka, face mulkin wariyar launin fata. Mutane biyu na zaune a kasa daya mutum guda yanada duk wani yanci a kasar, Kuma fa Ina magana ne akan kasarda aka mamaye. Mutane kala biyu na zaune a wannan kasar sashe daya na mutanen nada ko wane irin yanci a duniya,( sunada yancin yin komai) sashe daya Kuma basuda yancin yin komai. Yayi kama da mulkin mallaka, yana kanshin mulkin mallaka tabbas mulkin mallaka ne. Babu wani mutum mai adalci da zai je kasar ya duba irin arziki da yalwa dake tsakanin tsaunukan Jordan( wato Izraila) sannan a bangare daya Kuma ya duba kasar Falasdin da basuda ko wutar lantarki sannan yace ba mulkin mallaka bane ko yayi yunkurin kawo wani take na dabban. Idan har na saci motarka banida wani yanci na saka maka sharadin yadda zan mayar maka da motarka. Abuna farko shine in mayar maka da motarka a wannan misalin babu wata hanyar mayarda motar face bawa Falasdinawa yanci daidai da Yahudawa. "
Idan har akwai mutane masu gaskiya da tsoron Allah a kasar Izraila to Gideon Levi yana daga cikinsu. A matsayinsa na dan jarida mai sharhi akan kasar Falasdin a kafafen CNN, BBC Aljazira tabbas ba karamin jarumi bane har da zai iya wannan kasadar ya fadi gaskiyar abunda ya gani. Na jinjina mashi.
Da yawan mutane na kokarin kafa hujja da mummunan abun tsoron da ya auku ranar 7 ga watan Oktoba 2023 lokacinda dakarun mayakan Al Qassam na kungiyar Hamas suka farwa turawan mulki mallaka na Izraila da zimmar ramuwa akan mulkin mallakar da aka shafe shekaru ana masu, suka kashe Yahudawa sama da mutum 1000 daga ciki harda mata da kananan yara kana sukayi awon gaba da sama da mutane 200. Amma abun mamaki shine yadda masu kafa irin wannan hujjar suka manta da yadda Izraila ta kashe sama da Falasdinawa 700,000 a shekarar 1948 cikinsu harda mata da kananan yara kisan kiyashi da ake yiwa lakabi da Nakba.
Buga da kari tun daga wannan lokaci yau shekaru 76 kenan Falasdinawa a zirin Gaza dama yammacin kogin Jordan na fama da kisan gilla, handama da babakere daga hannun sojojin mulkin mallaka na kasar Izraila dama Yahudawa yan share waje zauna masu dauke da makamai. Dubban Falasdinawa ne maza da mata ke daure ba tare da sharia ba a gidajen yari na Izraila, sun manta yadda Izraila ta mayarda Gaza matsayin wani gidan kaso mai dauke da mutane sama da milyan 2.5 a mammatse kamar kifin gwangwani cikin kaskanci da tozartawa.
Kamar hakan bai isaba karmu manta da cewa a cikin shekara daya data gabata kasar Izraila ta kashe Falasdinawa fararen hula sama da 60,000 wudanda mafi yawancinsu mata ne da kananan yara, sannan kashi daya cikin mamatan suna karkashin kankaren gidanju daya zuba kansu sanadiyar kisan gillanda sojojin mulkin mallaka na Izraila nayi masu.
Ton 85,000 na bama bamai sojojin mulkin mallaka na Izraila suka harba zirin Gaza a cikin shekara daya, hakan yayi sanadiyar rushewa da ruguje kimanin kashi 75% na gine ginen zirin.
Bugu da kari kasar Izraila ta rushe duk wata Jami,a dake kasar Falasdin ta rushe kashi 95% na duk makarantu dake Falasdin ta kuma rushe duk Asibitin dake kasar face guda 13 kacal da suka rage a zirin na Gaza. A takaice babu sauran wani gari mai suna Gaza da ya rage.
Mata, kananan yara, jarirai, yan makaranta, yan gudun hijira, ma, aikatan majalisar dinkin duniya, masallatai, asibitoci, coci coci babu wani abu da Izraila ta dagawa kafa.
Kwanaki kadan da suka gabata tashar CNN ta ruwaito cewa:
" Kamar yadda rahoton kwamitin kare yan Jarida ya ruwaito akalla yan jarida 128 ne aka kashe kawo yanzu ( a yakinda Izraila ) keyi a Falasdin cikin shekara daya kusan dukansu Falasdinawane Kuma an kashesu ne sakamakon kai hari da jiragen yaki dake harba bamabamai. Wasu daga cikin yan jaridar an kashesu ne suna sanye da kayan aikin Jarida dake nunawa karara cewa yan jarida ne. Kafafen yada labarai da dama kungiyoyin jarida sun zargi sojojin Izraila da kai hari da gangan akan yan jarida.
Mutum zaiyi tsammanin cewa irin kisan gilla da kisan kiyashi da akewa abokan aikinsu a kasar ta Falasdin da kuma Lebanon a yanzu zai janyo hankalin gidajen jaridun yammacin duniya wajen bayyana irin ta,asa da kuma laifukan yakinda Izraila ke aikatawa a Falasdin, amma sun kasa fadar gaskiyar abunda ke faruwa, asali ma sun zabi su boye gaskiya su kuma bada kariya ga irin wannan kisan kiyashin da wariyar launin fata dake faruwa a gaban idonuwansu.
Wudanda a yau suke yabawa rashin imaninda Yahudawan Zionawa ke aikatawa a zirin Gaza, Yammacin kogin Jordan, Lebanon, Siriya, Yamen da Iran sun manta da cewa idan Yahudawan sukayi nasarar shafe wudannan kasashen da sukeda muradi, suka Kuma samu nasarar kafa gagarumar kasar Izraila da suke bukatar kafawa da jinin Musulmi, kirinsta da Larabawa to zasu juya akalarsu i zuwa sauran kasashen kudancin duniya ( Kasashe masu raunin tattalin arziki da kimiyya).
Wannan shine kalubalenda ke gaban mu a yau, dolene mu kafa sabuwar alakar soja da kuma tattalin arziki domin fuskantar wannan kalubale da kuma durkusheshi a duk lokacinda ya taso.
Duk da haka kafa gagarumar kasar Izraila ba shi bane kawai burin Yahudawa Zayonawa, bukatarsu itace su rushe duk wani babban addini a fadin duniya hadi da musulunci, kiristanci tare Kuma da kafa duniya akan turbar yahudanci.
Wannan shine muradinda suke bibiya ido a rufe, basuda wani buri daya wuce wannan idan kuma mutum na musu to ya karanta littafansu Talmud da kuma Torah.
Su karanta littafi mai suna " Protocol of the Elders of Zion" Wanda dukda irin farfaganda da karairayinda marubutan Yahudawa dama na yammacin duniya da yadawa sahihancin wannan littafin tabbatacce ne.
Tabbas duba da irin tsantsar rashin imaninda Yahudawan Zionawa ( Zionist) suke nunawa a kasar Falasdin shekara daya data gabata yana nuni da cewa kuskure mafi girma da duniya ta taba tafkawa shine aminta da kirkirar kasar Izraila a shekarar 1948.
Yunkurin da ya samo asali akan zimmar kare hakkin dan Adam, tausayi da yunkurin kawarda zaluncin da aka fuskanta a yakin duniya na biyu na nan ya kasance sinadarin yakin duniya na 3 da zai iya sanadiyyar kawo karshen bil Adama.
Tabbas wannan abun tunani ne.
Tabbas mutane da yawa na tantamar yancin wanzuwar kasar Izraila, bama zancen wai ta kare kanta ba.
Shin sojojin mulkin mallaka, yan share waje zauna, masu kisan kiyasa, azzalumai nada yancin ci gaba da kisan kare dangi da mulkin mallaka hadi da yunkurin shafe masu kasa daga doron duniya?
Shin zama farar fata na iya zama wani lasisi ga Yahudawan Ashkenazi dasu ci gaba da zubarda jinin Falasdinawa, Larabawa dama ilahirin gabas ta tsakiya?
Shin gaskiya ne cewa Yahudawa sune kadai tsabtataccen jinsin dayafi kowa a doron duniya, sunfi karfin dokar kasa da kasa Kuma basa laifi?
Shin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron baiyi gaskiya ba inda ya shawarci kasashen turai dasu daina sayarwa kasar Izraila da makamai?
Shin lokaci baiyi bane da kasar Amurka wacce ke taimakawa kasar Izraila wajen kisan kiyashi da kisan kare dangi a Falasdin ta farka daga baccinda take ta samu yancin kanta daga kasar Izraila da yan kanzagi dama fadawanta da suayi kaka gida a kasar ta Amurka?
Shin lokacinda Amurka zata sauya akalar kudurinta a duniya baiyiba, lokacinda zata takawa fadawan Izraila a kasar birki baiyi ba?
Wudannan muhimman tambayoyi ne da ansoshinsu zasu bayyana nan bada jimawa ba.
Wannan hakikanin abunda zai faru kenan duba da cewa Kashi 80% na Yahudawa Zayonawa mazauna Izraila sunki aminta da kudurin samarwa Falasdinawa kasarsu, sun buga Kai da kasa akan cewa Falasdinawa ba cikakkin mutane bane don haka suci gaba da zama cikin kaskanci da mulkin mallaka.
Idan har munason mu gane irin dakikikaci, sakarci da tunanin rashin imaninda ke zukatan mafi yawancin Amurkawa dangane da kasar Izraila, to yin la,akari da kalaman Tim Walz dan takarar mataimakin shugaban kasa tareda Kamala Harris a zabe mai zuwa a yayinda yake mahawara da J.D Vance satinda ya gabata yana mai cewa,
"Fadada Kasar Izraila ya zamo dole ga Amurka".
A lokacinda duniya ke kara neman tsagaita wuta da kuma samarda zama lafiya amma Amurka na zance fadada Kasar Izraila da zimmar gina gagarumar kasar Izrailar da Benjamin Netanyahu ke muradi, sam wannan ba kuduri bane da zai haifawa duniya da mai ido.
Kuyi man uzuri in rufe wannan sashen da nuna rashin amintata da irin yadda kasar Izraila ke tafiya tsawon shekara daya data gabata sannan kuma in fadi da babbar murya cewa kasar masu kisan kiyasa, masu kisan kare dangi da kuma handama da babakere bazasu taba yin nasara a kowane irin yaki ba.
Koba dade ko bajima zasu durkushe.
Abun dubawa ne irin yadda manyan yan jarida a kasar ta Izraila ke kara hango irin wannan makomar dake jiran Izraila, sakamon mummunan tafarkin zubarda Jin, handama da babakere da shugaban kasar Benjamin Netanyahu ya zabi yabi.
Misalai guda uku sun ishi mai hankali.
Kwanaki kadan da suka gabata Sher Hever, babban masanin siyasar tattalin arziki Wanda ya girma a Izraila yana cewa.
"Kisan kiyashinda kasar Izraila ke aikatawa a zirin Gaza abune da zai juyo kanta ya shafe ta ita da kanta, duk kasa ko al,ummarda ta maida zubarda jini al,ada to a karshe nata jinin zuba zaiyi saboda sharri kare ne".
Tabbas ya kasance mujiya mai hangen nesa, Kuma abunda ya hango baida ba makawar faruwarsa.
A nasu bangare kuwa babbar jaridar kasar Izraila wato Haretz ta ruwaito cewa.
Natenyahu ya tsunduma kasar Izraila cikin mafi munin shekara da kuma mafi munin yaki a tarihin kasar wanda har i zuwa yanzu ana Kai. Tarihin bazai taba tuna Benjamin Netanyahu ba a matsayin wani gwarzo daya jagiranci yammacin duniya wajen yakar wuce iyakar musulunci ba kamar yadda shi yake ganin kansa. Sabanin haka tarihi zai tunashi a matsayin wani shashashan dan siyasa daya jagoranci Izraila zuwa 7 ga watan Oktoba da duk sauran wata tabargaza data biyo baya".
Daga karshe a wani jawabinda aka wallafa a jaridar ta Haretz mai taken Izraila tayi numfashi na karshe wanda Ari Shavit wani shahararren dan jarida Kuma bayahude ( Zionist) ya rubuta yana mai cewa:
" Ga alama munyi nisa bama jin kira, mun wuce lokacin tunanin tsayarda wannan mulkin mallakar a samu zaman lafiya. Ga dukkan alamu lokacin hada kan al, ummar kasar nan ya wuce, lokacin gyaran zayoniyanci (zionism) ya shude haka ma lokacin gyaran demokradiyya ya kau".
Ya ci gaba da cewa,
" Babu wani amfanin ci gaba da zama kasar nan, babu wani amfanin ci gaba da rubuta a jaridar Haretz, babu wani amfanin ci gaba da karanta jaridar Haretz. Abunda ya rage mubi shawararda Rogel Alpher ya bayar shekaru biyu da suka gabata. Inda yake cewa abunda ya rage shine mu bar wannan kasar idan Izrailanci da Zayoniyanci sun gagara, idan kowanne dan kasar Izraila na rike da Fasfo din kasar waje to komai yazo karshe kenan. Lokaci yayi da zamuyi ban kwana mu kama hanya zuwa San Francisco, ko Berlin ko Farisa.
Ya ci gaba da cewa.
" Dole ne mu matsa baya mu kalli yadda kasar Yahudawa mai ikirarin Demokradiyya zata ruguje, mai yiyuwa bakin alkalamin bai kai ga bushewa ba, mai yiyuwa lokacin bai kure ba. Mai yiyuwa akwai yiyuwar kawo karshen mulkin mallakar, a kawo karshen share wuri zauna, a tsabtace zayoniyanci ( Zionism) a Kuma raba kasar ( Tsakanin Yahudawa da Falasdinawa).
Ya rufe bayaninsa da wudannan kalmomin,
" Ga dukkan alamu mun hadu da mutanen da suka fi kowa jajircewa a tarihi, mafita daya itace mu basu yancinsu mu kawo karshen mulkin mallakar".
Sher Hever, Edita a jaridar Haretz da Ari Shavid sun fito da tunanin milyoyin yan kasar Izraila a yau.
Idan irin wudannan kalamai na fitowa daga kasar Izraila babu shakka akwai zaton mulkin zalunci da tumasancin Benjamin Netanyahu ya fara fuskantar barazanarda zata kawo karshen sa. Saura kiris ya rugurguje daga ciki.
Muna fatan wannan shine abunda zai afku domin kuwa abunda zai faru idan hakan bai faru ba to zai kasance mafi muni, kuma zai iya janyo shafe kasar Izraila daga ban kasa.
Hakikanin gaskiya shine idan akwai wani kalubale dake barazana ga wanzuwar kasar Izraila to ba Falasdin bace, ba Iran bace ba Hizboullah bace, ba Houti bane ba Larabawa bane ba kowa bane face Benjamin Netanyahu dashi da mukarabbansa da yan anshin shatansa dake yunkurin rura wutar yakinda zai iya kawo karshen kasarsu ba zancen suyi nasara ake ba.
Kuyi man uzuri, zan karasa da wannan.
Giorgia Mitralias dan jaridar kasar Girka, yana mai cewa a cikin wani sharhi mai taken " A Lokacinda abokan cin mushen Izraila suka da,i,mantar da zalunci, alfasha da fasadi a bayan kasa.
Yana cewa,
" Kusan shekara daya kenan da muka rubuta cewa daya daga cikin muradun Natenyahu tareda da abokan cin mushen sa shine su mayarda duniya kamar wani jeji wanda babu wata doka face zalunci da fin karfi, inda za,a halattarda zalunci, fin karfi da kuma handama da babakere.
Yau kimanin watanni 12 laifukan yaki, zubarda jini da kuma zaluncinda suke aikatawa yama wuce inda muke tsammani, zamu iya cewa kasar Zayonawa ta saba wa duniya da mafi munin abunda mukayi zargi dangane da kisan fararen hula, kisan kiyashi, yada fasadi da husuma, kin gaskiya, da rashin rike alkawali. Sun dabbakawa duniya sabo da wudannan mummunan laifukan yaki da suka kunshi zubarda jinin fafaren hula da basuji ba basu ganiba dama daukar hakan kamar ba wani laifi ba. Tabbas akwai jini a hannu duk Wanda ya gani ko yaji amma dauki abun kamar ba komai ba, ba wai sai Wanda ya aikata laifin ba kawai. Tabbas akwai jini a hannu duk wani Wanda ya gani yayi kamar bai ganiba harma da kara basu goyon bayan ci gaba da aikata wudannan mummunan laifuka.
Giogus ya fadi gaskiya mai daci: tabbas duniya ta rasa tausayinta da kuma imaninta,
Allah mana kariya.
Femi Fani Kayode, Sadaukin Shinkafi.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma tsohon ministan Al adu da yawon bude ido tarayyar Najeriya.
Tags
Hausa