Shin Wane irin Tsibbu da Bori ne ya Mallake Sha Lelen Duniya Amurka?

Daga Cif Femi Fani Kayode

Nakanyi matukar alhini da juyayi a duk lokacida na tuna da irin gwagwarmaya da sadaukarwa jaruman Amurkawa na wancan lokacin sukayi domin kafa gagarumar kasar ta Amurka, da yadda suka sadaukarda kawunansu da rayuwarsu a lokacinda suke yakar gwamnatin mulkin mallaka ta Burtaniya a shekaru 1776. Mutane kamar su Gorge Washington, Thomas Jefferson, John Adams, Benjamin Franklin da dai sauransu. Shin sun taba yin tsammanin cewa abunda ke faruwa a Amurka a yau zai taba faruwa a kasarda suka sadaukarda komai nasu domin tabbatuwarta?

Na kanyi mamaki idan jajirtattun iyayen nan da akewa lakabi da mahajjata a can baya, da suka baro tsohuwar duniya suka tsallake tekun Atlantic cikin rintsi, hatsari, yunwa da sauran wahalhalu suka tsallaka har sabuwar duniya inda suka samarda wata kasa ta musamman akan Falsafar tsoron Allah, da kuma ginshikin addinin ( Nasara) kiristanci na gaskiya, suka sadaukarda kawunansu wajen roko ga mahalicci suka kafa kasar ta Amurka akan turbar gaskiya da adalci. Nakanyi alhini duba da irin yadda wannan kasar ta kasance a ayau, shin da suna raye da ya zasu ji?

Anya kuwa basa juyayi a cikin kaburburansu?

Kasar da tayi fice wajen tabbatarda yanci da jarunta a yau ta kasance cikin batan bakatantan ba yancin kuma ba jaruntar. 

Gagarumar kasar da tayi fice wajen yaki da zalunci, kasarda ke alfahari da tabbatarda kare hakkin dan Adam da kuma yancin fadan albarkacin baki, kasarda ta shafe shekaru tana yaki domin ganin an kawarda bauta a kasar ta Amurka da zimmar gina wata gagarumar kasa da duk bil,adama zasu kasance masu yanci, da kawarda wariyar launin fata, da banbancin addini amma yau ta samu kanta cikin wani halin mulkin kama karya, handama da babakere hadi da tumasanci a hannun shuwagabanni da suka sayarda duk wani yancisu dana yan kasarsu suka koma yan anshin shatan kasar Israela da yan kanzaginta a karkashin kungiyar AIPAC. 

Gagarumar kasar da ta taimaki duniya wajen kawo karshen yakin duniya na daya dana biyu, kasarda taci galabar kwamunisancin Rasha dake barazana ga duniya a wancan lokacin ta habbaka mulkin demokradiyya a fadin duniya, kasarda ta kafa daula mafi karfin mulki da karfin soja a bayan kasa a wannan qarni ace ta koma yar kanzagin kasar Israila?

Gaskiya abun da kamar wuya, amma kuma gaskiya ce. 

Kamar yadda shedan ya rinkito daga matsayinsa haka kema Amurka Zaki antayo. 

Kaicon ki Amurka. 

Bayan tabarbarewar harkokin mulki da na siyasa, kun gurbata addini kun maidashi ba bakin komai ba, kun halatta luwadi da madigo, kun halatta zubarda ciki, kun koma bautar shedan da kyalekyalin duniya. Kun kawarda duk wani hukunci na Allah, kun wofantarda tare da cire duk wani karatun addini ko tarbiyya a makarantunku da zimmar kafa sabuwar duniya. Da taimakon yan kanzaginku kamar Burtaniya, Faransa, Jamus, Holland da sauransu kun wargaza duk wani yunkurin kawo ci gaba a wasu kasashe ta hanyar handama da babakere. 

Jerin kasashenda kuka rugurguza mai tsawo ne sosai, kadan daga cikinsu sun hada da Libya, Syria, Yemen, Afghanistan, Somalia, Lebanon, Sudan, Palestine, Ukraine da sauransu. 

Kun rugurguza su, kun mayarda su kufai, kawai saboda kunyi niyar batarda su kamar yadda kuke batattu amma sun bijire maku sunki yi maku mubayi,a. 

Yanzu a haka kuna yunkurin aikata abunda kuka aikata a wasu kasashen a Rasha, Sin, Iran, Korea ta Arewa, Turkiyya, Pakistan, Indiya, Africa ta Kudu, Kasashen Gulf na larabawa, Brazil, Niger, Chadi, Burkina Faso, Mali, Najeriya, Ethiopia, Senegal, Gini, Masar, Algeria da sauransu. 

Kunayin hakan ne da zimmar mulkin kama karya, handama da babakere amma alhamdulah bakuyi nasara ba. 

Daga bisani irin yadda kuka daurewa mulkin mallaka gindi, kuka yi amfani da dukiyar kasarku ba tare da amincewar yan kasarku ba wajen tabbatarda ci gaban mulkin mallaka da wariyar launin fata shine ya nuna asalin halinku na munafunci, boye gaskiya da kuma son zubarda jini. 

Kun kasance masu taimakon mulkin mallaka, kisan kiyashi, kun rufe idonku wajen taimakon kasar Israila ta ci gaba da zubarda jinin mata da kananan yaran Falasdinawa da zimmar kawardasu daga bayan kasa.

A cikin watanni bakwai da suka gabata kun saka duniya cikin alhini da kuma rudani irin yadda kuka kyankyashe idonku kuke taimakawa kasar Israila wajen tabbatarda kisan kiyashi da kisan kare dangi a zirin Gaza, kun bijirewa duk wata dokar kasa da kasa inda kuke azabtarda Falasdinawa ta hanyar kisan kiyashi, wariyar launin fata da kuma kisan kare dangi. 

Wannan ba abun a aminta dashi bane, Kuma alhakin zubarda jinin bayin Allah da basuji basu gani ba na wuyanku daku da kasar Israila. 

Tabbas Israila bazata samu karfin guiwar tabbatarda irin wannan mummunan aikin ba tareda goyon baya da kuma hadin bakinku ba. 

Tabbas wannan mummunan aiki ne kuma abun kyama, amma abunda ya fishi zama abun kyama shine a duk lokacida kasashen duniya suka yi yunkurin hukunta kasar ta Israila saiku dage kiri da muzu ku basu kariya harda yin barazana ga duk wani mai niyyar tabbatarda adalci ko kawarda mulkin wariyar launin fata da kisan kiyashi da kuka daurewa gindi. A yau da goyon bayan ku kasar Israila ta zamo kasarda tafi karfin doka da zata iya karya ko wace irin doka ta zauna lafiya. 

Wannan tsantsagwaron rashin adalcin, kin gaskiya da goyon bayan kisan gilla da kisan kiyashi wata manuniya ce akan irin yadda kuka zamo. 

Bakwa tsoron Allah, baku tsoron bakin mutanen duniya gaba daya Kai bama ku tsoron fushin al,ummarku dake zangazangar nuna kyamar mummunan aikinda kuke goyon baya. 

Iya abunda kuke tsoro itace uwar gijiyarku kasar Israila.

Wannan ne dalilinda yasa nake tambayar ku, shin wane bokane ya mallakeku, wane irin tsafi, bori da siddabaru ne ya hau kanku. Shin wane irin asiri yahudawa suka yi maku. 

Kun shagala, kun zubarda kimarku a idon duniya, kun tashi daga matsayin ku na masu fada a ji a Siyasar duniya kun koma abunda yan Najeriya ke kira da yan daudu kuma yan anshin shatar kasar Israila. 

Da zarar an ambaci sunan Israila zuciyar Amurka ke kadawa, kwarkwatarta ta dugunzuma, ta rikirkice kamar wata tsohuwar sarka, tai tamkar dai saurayi a gaban budurwarsa yar kwalisa. 

Tabbas wannan aikin shedan ne, an riga an mallakeku an tsibbance ku, baku cikin hankalinku, wani mummunan shedani ne ke tafiyarda tunani da ayyukanku. 

Kaicon ku.

Duk lokacida Kotun kasa da kasa akan laifukan yaki ta ICC ta bada damar kama wani Shugaba akan wata tabargaza kune kan gaba wajen yayataw da farfaganda amma yanzu da kotun ke kudurin bada damar kama ubangidanku Firam ministan Israila Benjamin Netanyahu duk kun rikirkice, kun tsure, kunata sambatu haba Amurka. 

Ta hanyar wani dan kanzakinku a gwamnatance harda ikirarin cewa kotun ta ICC bata da hurumi ko damarda zata bada dokar kama Benjamin Netanyahu. 

Kun manta da cewa kune ke rawa da guda lokacinda ita wannan kotun ta bada damar a kama shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. 

A wancan lokacin kun yi amanna da cewa kotun ta ICC tayi daidai kuma tanada hurumin bayarda dokar a kama Putin amma da zancen yazo kan Netanyahu sai zancenku ya canza. 

Kalar munafuncinku bashi da misali.


Bayan haka kun kakabawa yan kasarku wata sabuwar doka wadda taci karo da kundin tsarin mulkinku wai da zimmar haramta kin jinin Yahudawa, wannan dokar karara ta sabawa yancin dan Adam na fadin albarkacin bakinsa da kuma yunkurin daure duk wani wanda ya kushe kisan kiyashi da Israila keyi, koya ambace wariyar launin fata da sukewa Falasdinawa Kai ma har a ko ina a cikin tarihinsu na shekaru 5000 da suka gabata harma da maimaita ababenda aka fada a cikin littafi mai tsarki na Bible. 


Majalisarku ta haramta misalta abunda ya faru da Yahudawa a karkashin mulkin Nazi a kasar Jamus da irin abunda yahudawa ke aikatawa Falasdinawa a yau dukda cewa ko makaho yasan suna kamanceceniua da juna. A takaice dai kun haramta karanta Bible a matsayinku na kirista. 

Shin wannan ba wata manuniya bace ta tabin hankali?

Dokar ta kuma haramta karanta sassa dabban dabban na Bible dake bayani akan irin tabargazarda yahudawa suka aikata shekaru aru aru da suka gabata!

Haka ma majalisar wakilai ta yi zabe akan hana yin waa,azi da Bible daga farko zuwa karshe, saidai a zabi sassa da basu fadi tabargazarda yahudawa suka aikata ba. Shin wannan ba an haramta addinin kiristanci bane a kasar Amurka?

Kuyi tunani. 

Jaridar Megatron_ron ta bayyana hakikanin abunda ke faruwa a shafinta na manhajar X data ruwaito kamar haka.

" Majalisar kasar Amurka ta rattaba hannu akan wata doka data haramta suka da kushe kasar Israila. Harma idan ka karanta sashen Bible da yayi bayani akan yadda yahudawa suka kashe almasihu to za,a daureka. Sannan kuma akan zangazangar lumana da yan makaranta keyi a fadin kasar majalisar na shirin rabbata hannu a kan wata doka mai taken HR 6090 wannan dokar zata fassara kin jinin yahudawa sannan kuma zata baiwa gwamnatin tarayyar Amurka damar shigarda kara, hukuntawa da kuma saka takunkumi ga daidaikun mutane, kamfanoni dama makarantun gaba da firamare akan laifin sukar Israila ko yin zanga zanga akan abunda take aikai. Ko a zargi yahudawa da laifin wariyar launin fata, da kuma zargin yan kasar Amurka da cewa sunfi yiwa kasar ta Israila biyayya fiye da kasar Amurka. 

Shin wannan ba abun alhini da bakin ciki bane?

Shin wannan ba abun bakin ciki bane na bugawa a Jarida?

Shin wannan bai sanya zuciyarku dugunzuma ba?


Shin mun shigo duniyarda shahararren marubucin nan Gorge Orwell dan kasan Ingila yayi hasashe karnuka da yawa da suka shude ko kuma yadda David Dicke yayi hasashe?

Anya Amurka kasarda tayi fice wajen tabbatarda gaskiya da adalci bata rasa wannan matsayin ba ta hanyar komawarta yar anshin shatan kasar Israila?

Tabbas bazamu sake kira ta da hadaddiyarJahohin Amurka ba, saidai da lakabin hadaddiyar kasar Zion. ( United States of Zion)

A nashi bangaren @jakeshieldsajj mai sharhi akan harkokin yau da kullum Kuma dan kasar Amurka a shafinshin na manhajar X cewa yayi: 

" A cikin sati biyu da suka gabata majalisa ta kafa dokar haramta kushe duk wani abu da kasar Israila ta aikata, ta haramta zangazangar lumana akan Israila, ta haramta amfani da manhajar TikTok kamar yadda Israila da bukata, sun bada kyautar kudi har dala bilyan $100b ga kasar Israila da Ukraine domin suci gaba da yaki, sun bawa bakin haure bilyan $3.5b a matsayin tallafi, ba tareda sunyiwa yan kasar Amurka wani abun azo a gani ba. Wannan wata mahanga ce mai nuna cewa bamu sukazo suyiwa aiki ba. 

Jake ya fadi gaskiya mai daci. 

Maiyiyuwa mafi munin furuci a cikin wannan cecekucen ya fito ne daga bakin Senator Ted Cruz, tsohon dan takarar shugaban kasar ta Amurka wanda kafin yanzu nake matukar girmamawa. Inda yake cewa. 

"Bana Allah wadai da duk wani abunda kasar Israila ta aikata"

Don Allah wannan ba alamar tabin hankali bace?

Ana kashe mutane kamar kiyashi, dubban mutane na mutuwa a kowane wata, ana kashe mata da kananan yara da makaman da kasar Amurka ke aikawa Israila amma a matsayinka na dan majalisa kace baka Allah wadai da haka?

Shin wannan bai sanya Cruz ya kasance da alhakin zubarda jinin bayin Allah da ake a zirin Gaza ba?

Ted Cruz da makamantan sa su bani dalili guda daya cak da zai sa inyi Allah wadai da abunda Hamas suka aikata a 7 ga watan oktoba idan bazaiyi Allah wadai da Nakba da Israila ta aikata a shekarar 1948 ba inda suka kashe kusan Falasdinawa milyan daya!

Su gayaman dalilinda zaisa inyi Allah wadai da Hamas idan basuyi Allah wadai da abunda kasar Israila ta aikata ba a shekarar 2024 inda suka shafe watanni 7 suna ruwan bamabamai dayayi sanadiyar kashe farar hula 40,000. 

Sannan Ted Cruz dashi da sauran abokansa a majalisa na ikirarin cewa furucin da Falasdinawa ke amfani dashi na cewa " daga teku zuwa rafi Falasdin zata samu yanci" wai wata manuniya ce akan kudurin Falasdinawa na shafe duk wani bayahude daga ban kasa. Amma saboda tsantsar munafunci sunki suyi ce hakan lokacinda yahudawa ke amfani da furucin wajen cewa " daga rafi zuwa teku Israila zata samu yanci"

Shin meya kawo wannan munafuncin?

Idan Falasdinawa sukayi wannnan furucin saikuce sun fada ne da zimmar kawarda duk wani bayahude daga bayan kasa amma idan yahudawa suka fadi hakan saikuce ba sun fada bane da wata mummunar niyya. 

Shin wannan ba wata mummunar akida bace wadda ta dauki Falasdinawa da cewa basu Kai matsayin mutane ba, amma aka dauki yahudawa kamar wasu ababen bauta ba?

Shin akwai adalci anan? Akwai zancen hankali anan?

Yahudawa sun kasance kashi biyu 2% a cikin 100 na yan kasar Amurka amma sun zamo yan lele Amurka, an basu damar karya ko wace irin doka sukaga damar karyawa, haka kasar Israila mai mutane milyan 9 ta zamo kamar wata kasar ababen bauta. Sunfi karfin doka, an basu damar aikata duk abunda suka ga dama ba tareda hukunci ba. 

An bawa kasarda tafi kowace kasa a tarihi aikata laifukan yaki damar ci gaba da aikata mummunan laifukan kisan gilla, wariyar launin fata, hadi da giciye Yesu almasihu shekaru 200 da suka gabata. Kasarda a tarihi ta kashe Amalekawa 5000, Madayyanawa 4000, Agagawa 3000 daga bisani suka kashe Falasdinawa milyan daya a 1948, daga bisani sukayiwa dubban larabawa kisan kiyashi shekaru 75 da suka gabata gashi a yau sun kashe Falasdinawa 40,000 a cikin akwai kananan yara 20,000 a cikin watanni 7 da suka gabata gashi Kuma suna shirin shiga birnin Raffa da zimmar ci gaba da abunda suka Saba.

Shin wannan ba hauka bane? Ba tabin kwakwalwa bane? Ku bani ansa wane irin sammu ko tsibbu ne ya mallakemu?

Nayi tir da halinku!

Karfin mulkinku da tarin dukiyarku ya kaiku ga halaka, kun ratse daga hanyar tsira Kun bi shawarar shedan. 

Daga jagorancin adalci da yancin biladam Kun kasance yan ashin shata masu goyon bayan wariyar launin fata, kisan kiyashi, handama da babakere. 

Gaskiyar itace babu wata hujja da zata bada kariya ga irin wannan mummunan aikin na kashe mata da kananan yara. 

Kasar Zayonawa ta Israila itace hatsari mafi muni da ya shafi duniya tun bayan kawarda gwamnatin Nazi a kasar Jamus. 

Ta kasance wata kasa ta yan kama karya, handama da babakere hadi da rashin Imani wacce ta wofantarda yancinta na wanzuwa. 

Tabbas ta cancanci a shafeta daga doron kasa domin duniya ta samu zaman lafiya. 

Dukda haka a Amurka akwai tsammanin canji, duba da irin yadda kiristoci yan makaranta ke zangazangar lumana da zimmar kawo sauyi. Kamar yadda Yan makaranta suka hana yammajalisa shiga gidan abinci satinda ya gabata suna masu cewa idan har mutanen zirin Gaza basu samu sunci abinci ba to suma yan makarantar bazasu bar yan majalisar su shiga gidan abincin ba ballatana har suci wani abun. 

Tabbas wannan zaton sauyi yana kan dalibai yan makarntar da suka sha alwashin tabbatarda gaskiya da kuma kare hakkin dan Adam. 

Kamar yadda tsohon dan takarar shugaban kasar ta Amurka Senator Bernie Sanders ya fada a jawabinsa ga yan makarantar yana mai cewa " suna fito saboda muradi na gari, basu fito da zimmar goyon bayan kungiyar Hamas ba, sun fito ne saboda suna bakin cikin abunda gwamnatin Israila ke aikatawa a zirin Gaza. "

Tabbas Sanders ya fadi gaskiya, kuyi man uzuri in Kara da cewa tabbas wudannan yan makarantar sune mafita ga kasar ta Amurka. 

Dukda cewa jami,an tsaro na yunkurin murkushesu, da kuma yunkurin dukufarda dasu da toshe muryarsu sun nuna bajinta da jajircewa. Sama da dalibai 2000 ke tsare a gidajen kurkuku mabanbanta domin nuna kin goyon bayan kisan kiyashi da akewa Falasdinawa a zirin Gaza. 

Tabbas sun kasance abun alfahari ga kasar Amurka, a yau kuwa duk sun harzuka sun cika tituna suna zangazangar lumana da nuna goyon bayan Falasdinawa.

Tabbas wannan wani muhimmin sauyine a tarihin duniyar mu. Zuciyoyi da hankulan matasa sun hade waje daya da zimmar kawo karshen mulkin mallaka da fuskantar shugabancin kasarsu da kasar Israila ta mallake tun bayan yakin duniya na biyu. 

Kuyi man uzuri inyi tsokaci daga karshe kamar haka. 


Babu wani abu daya sanya nishadi fiye da irin sauyin da muke gani kamar kalaman Farfesa Rashid Khalid Wanda ya kasance Farfesa a fannin yaren larabci a jami,ar Columbia dake birnin New York. 

A wani jawabi da zai kasance wani Kari a kundin tarihi farfesan yana gayawa yan makarantar cewa. 

" Wannan kisan kiyashi ne da ake aikatawa da kudin Amurka, da makaman Amurka akan mutanenda suka shafe shekaru aru aru a karkashin mulkin mallaka. Yan makarantar Columbia sun kawo karshen yakin Viet Nam shekaru da yawa da suka shude a lokacinda nake dan makaranta mun kawo karshen wancan yakin, a yau Kuma muna tunawa da irin wancan namijin kokarin a yayinda muke gwagwarmaya akan kare hakkin Falasdinawa da mutanen zirin Gaza. 


Ubangiji Allah ya taimakesu, ya kuma bawa mutanen zirin Gaza nasara!

Cif Femi Fani Kayode, Sadaukin Shinkafi Kuma wakilin Doka Potiskum, tsohon ministan sufurin jiragen sama Kuma tsohon ministan Al,adun kasar Najeriya ne ya rubuta. 

Mohammed Bello Doka ya fassara daga turanci zuwa Hausa.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post