Rubutawa: Mohammed Bello Doka
Jakadan kasar Falasdin a Najeriya Abdallah M. Abu Shawesh yayi kira ga matasan Najeriya dama Afrika baki daya da su shiga su kuma bada gudumawa akan sabuwar Intifada data mamaye duniya a cikin yan kwanakin nan.
Mr. Abu Shawesh yayi wannan kiran ne a lokacinda yake ansa tambayoyi daga manema labarai a Ofishin jakadanci kasar ta Falasdin dake birnin Abuja.
Abdallah yayi kira ga matasan Najeriya da su yi koyi da takwarorinsu na yammacin duniya da ke zangazangar lumana a jami,oin yammacin duniya inda suke kira ga shuwagabannin su da su kauracewa Israila tareda kakaba mata takunkumi akan irin kisan kiyashi da kisan gilla da suke yiwa Falasdinawa.
Matasan na zangazangar lumana ne a jami,oi dabban dabban a kasashen turai da Amurka domin nuna kin jinin kisan gilla da Israilar ke aikatawa. Jakadan ya kara da cewa wannan irin yunkurin yayi matukar tasiri wajen kawo karshen yakin Viet Nam shekaru da dama da suka wuce, haka zalika zangazangar lumana ta yan makarantun jami,a tayi tashiri wajen kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar Afrika ta Kudu.
Abu Shawesh ya yi kira da matasan Najeriya dama Afrika baki daya dasu shiga wannan intifadar ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta wajen yada manufa da kuma yakar mulkin mallaka da wariyar launin fata.
Abdallah ya kara da cewa idan har aka kyale kasar Israila taci gaba da karya duk wata doka ta kasa da kasa to babu wanda yasan inda abun zai kare, yace idan yau Falasdin ne to gobe abun ka iya fadawa kan kowa.
Kawo yanzu sojojin mulkin mallaka na yahudawa tare da taimakon kasar Amurka da sauran kasashen turai sun kashe sama da Falasdinawa 34,789 sun kuma jikkata sama da 78,204 wudanda mafiyawancin su mata da kananan yara ne.
Kasar ta yahudawa ta kasance bata biyayya ga duk wata doka ta kasa da kasa, a yanzu a haka takai hari a kasashen Lebanon, Iran, Siriya da Yaman. Idan har aka barta Babu wanda yasan inda abun zai kare, don haka Jakada Abu Shawesh yayi kira ga matasan Najeriya dama Afrika baki daya dasu dage su hada karfi da karfe su kuma shiga Jerin gwanon sauran matasan duniya musamman na yankin turai da Amurka wajen kawo karshen wannan kisan kiyashin.