Shugabar Matan Jam,iyyar APC ta Taya Musulmi Murnar Fara Azumin Watan Ramadan

Mohammed Bello Doka

Shugabar matan jam,iyyar APC Dr. Mrs. Mary Alile ta taya ilahirin musulman Najeriya dama duniya baki daya murnar fara azumin watan Ramadan, inda tayi kira ga musulman da suyi koyi da kyawawan halayen fiyayyen halitta annabi Mohammadu SAW a cikin wannan wata mai tsarki. 

Shugabar ta kuma yi kira ga musulman cewa suyi amfani da wannan dama wajen yiwa kasa Najeriya adduoi, dama shuwagabanninta tana mai cewa lokacin Ramadan lokacine da ya kamata mutane dubi kawunansu tare da yiwa kansu hisabi akan alakarsu da kuma mu,amalarsu da mahalicci. 

Ta kuma yi kira ga yan Najeriya dasu hada karfi da karfe wajen yiwa kasa addua da kuma yin aiki tukuru domin kawo ci gaban kasa da al,ummar ta. Tana mai cewa lokacin Ramadan lokaci ne mai matukar muhimmanci ga rayuwar al,umma. 

Dr. Mary ta kara da yiwa musulman Najeriya fatan nasara tana mai addua akan Allah ubangiji daya karbi adduoinsu ya kuma basu nasara. Daga karshe ta kara da yin adduar nasara ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na cimma burinsa na sabunta zaton yan Najeriya. 

📸 *CAPACITY MEDIA HAUSA*

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post