Yadda Shugabar Matan Jam,iyyar APC ta Cinye Biki a Auren Yar Gwamnan Kebbi

Mohammed Bello Doka

Biki ake na manyan mata, wannan shine take da salon bikin dake faruwa a jahar Kebbi a daidai lokacinda masu ruwa da tsaki da kuma wane da wance na kasar nan sukayi dandazo domin taya Gwamnan Jahar ta Kebbi  Nasir Idris Kauran Gwandu murnar bikin auren yarsa. 

 *CAPACITY MEDIA* na bibiyar wannan gagarumin biki da ya samu halattar masu ruwa da tsaki na ciki da wajen kasan nan daga sassa dabban dabban. 

 *CAPACITY MEDIA* ta hanko Dr. Mary Alile wato shugabar matan jam,iyyar APC ta kasa tare da sauran mambobin Majalisar Zartarwar jam,iyyar kai harma da jagoran kungiyar na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje. 

Dr. Mary da tawagarta na ci gaba da gwangwajewa tareda shanawa a wannan biki, haka kuma yan uwa da abokan arziki na ci gaba da hallara domin ziyartar wannan gagarumin biki. Ku biyomu domin samun cikakken bayani akan yadda wannan biki ya kasance. 

 *CAPACITY MEDIA HAUSA*

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post