By Mohammed Bello Doka
A daidai lokacinda zaben Gwamnoni ke kara matsowa a jahohin Ondo da Edo, shugabar matan jam,iyyar ta APC na kara dage damtse wajen ganawa tareda hada kan masu ruwa da tsaki domin cimma nasara a zabukan masu zuwa.
A kan wannan maudu,in ne Dr, Mrs. Mary Alile ta karbi bakuncin wasu shuwagabannin mata daga jahar Edo da suka hada da Ambassador Betty Okuebor shugabar matan jam, iyyar APC ta jahar ta Edo kuma shugabar kungiyar shuwagabannin mata na jahohin Najeriya a karkashin jam,iyyar ta APC.
Mrs. Sandra Aguebor mace bakanikiya ta farko a Najeriya ma ta samu hhallattar wannan taron, sai Gimbiya IZ Jimoh mai taimakawa ta musamman a ofishin shugabar matan ta NASA da kuma shugabar matan APC na karamar huukumar mulki ta Oredo a jahar ta Edo da ma suransu.
*CAPACITY MEDIA HAUSA*