" Bayan ƴan rakiya sun raka ni gida na, muna shiga, sai mu ka tarar ba kowa a falo sai amarya, fuska rufe da mayafi, bisa al'ada. Ƙawayen amarya da ƴan rakiya duk sun tafi.
Wani abokina ya doka sallama, amarya shiru ba ta amsa ba, dama ni na sani kunya ba za ta bari ta amsa ba.
Nan dai mu ka zauna akan sabbin kujeru masu laushi, a zuciyata na ce "Yanzu fa wai nan gidana ne, daga yanzu wannan kayan alatu da aka jibge..."
"Sai mu yi addu'a mu yi musu nasiha, mu tashi mu tafi ko, wallahi duk jikina ciwo, ga dare ya yi, yanzu fa ƙarfe goma!" Wani cikin abokanai na ya katse mun wannan tunani.
Nan a ka yi addu'o'i da nasihohi, kamar yadda dai aka saba ba, bayan sun kammala, na rako su waje, na ja ƙofar gida na rufe.
Na dawo falo na tarar amarya fuska rufe, nai sallama na je dab da ita na cire mayafin da ke rufe kan fuskarta, ta ɗago kai ta kalleni, sai na ga ta zazzaro idanu, tana mun wani irin kallo kamar ranar ta fara gani na. Na ce "Tashi mu je mu yi alwala mu yi sallah ko?"
Nan fa amarya ta zabura ta miƙe, ta yi nisa da ni, kamar ta ga wani dodo, abin ya cika ni da mamaki ƙwarai, sai dai yanzu da na ga ta miƙe, sai na ga kamar dai ta ɗan ƙara tsayi, sannan kamar ta ɗan ƙara ƙiba. Ba kamar yadda na san ta ba, sannan fuskarta ma kamar ta canza, sai na yi zaton wannan kwalliyar da ake baɗe fuska da fenti ne ya janyo haka.
Cikin mamaki "Na ce Amira lafiya dai? Alola za mu je mu yi, amma bari in je in fara yi tukun, sai ke ma ki je ki yi ko?" Na cire babbar riga na shiga banɗaki na yi alola, ina ta mamakin Amira amaryata, a zuciyata na ce "wai dama haka wasu amaren su ke, ko dai tawa ce ta daban?" Bayan na fito na tarar da ita a cen gefe, a tsaye, na ce "Je ki alwala kin ji amaryata!"
A karon farko ta ce "Ni fa ba amaryarka ba ce, kuma ni ba sunana Amira ba" Sai na yi zaton ko da wasa ta ke mun, don na san ta akwai zolaya da wasa da barkwanci, na nufi inda ta ke, sai na ji ta ƙwala ihu, ta na cewa "Kar ka matso kusa da ni!" Duk na kiɗime, a zuciyata na ce "Ko dai aljanu ne da ita? Dama fa an ce wani zubin sai a daren farko su ke tashi, gaskiya in haka ne iyayen Amira sun cutar da ni.
Ihun da ta ke yi, ashe maƙota sun jiyo, duk a tunaninsu ko ɓarayi ne su ka shigo mana gida, nan fa aka yi dafifi a ƙofar gidana, akai ta buga ƙofa in buɗe, wasu kuma na ta ƙoƙarin haurawo don su kawo taimako, duk aka raba mun hankali, ga ihun Amarya ga hayaniyar maƙota a waje, nan na buɗe ƙofa, Amarya ta fito daga gidana a guje da ƙyar mata su ka riƙeta, tana cewa "Wallahi ba miji na ba ne!"
Ni kuma ina ta cewa "Wallahi matata ce, aljanunta ne suka ta tashi" abu ya rincaɓe, ana haka sai ga wata mota ta durfafo layin gidana a guje, suna zuwa, wani ya yi sauri ya fito daga cikin motar, ya ce "Ba matarsa ba ce, wajen kawo amarya ne aka samu kuskure, a wajen Titin Tal'udu aka samu matsala, convoy ɗin ɗauko amare ya rikice, mu amaryar nan ta mu ce, ta ku tana cikin mota"
Sai a lokacin aka fahimci yadda lamarin ya kasance, da ya ke an ɗaura aure da yawa jiya a Kano, to wajen ɗauko amare ne abu ya rikice, ni da za a ɗauko mun amaryata daga Kurna a kawo mun ita Ja'en sai aka samu matsala a nan Tal'udu, aka ɗauko mun wata amaryar wani da aka ɗauko daga Rijiyar Zaki zuwa Hotoro"
Mukhtar Mudi Sipikin
Tags
Hausa