Hon. Emwinghare K. Osabuohien
Tikitin takarar Gwamna a karkashin jam,iyyar APC ba gadon kowa bane, wata alfarma ce da ta kadaida ga cancanta, sadaukarwa da kuma himma. Tabbas Demokradiyya na samun habaka ne idan aka samu shuwagabanni ta hanyar cancanta da dacewa sabanin sanayya ko kusanci da madafun iko.
Wannan itace alkiblar APC kuma itace manufar mu. Irin kalubalenda jaharmu ke fuskanta yasa jaharmu na bukatar shugaba jajirtacce, ingantacce kuma sadauki.
Tabbas wajen share fage APC na bukatar cancanta fiyeta bangaranci, kabilanci ko wariyar addini. Muna bukatar samun dan takara da zai iya fitarda jaharmu daga halin waini yasu data samu kanta a ciki.
MAQASUDIN RAGE YAWAN YAN TAKARA GABANIN ZABEN FIDDA GWANI.
Takaice yawan yan takara gabanin zaben fidda gwani na jam,iyyar ta APC zaiyi maktukar taimakawa wajen rage rigingimu dayawa da ka iya tasowa, zai taimakawa jam,iyyar dama yan jam,iyya wajen samun natsuwa da kuma saukakawa wajen ayukkan zabe ya kuma bawa masu zabe damar samun cikakken bayani akan yan takararsu.
Wannan bashi bane lokaci na farko a jaharmu ta Edo ake zaunawa a tattauna a rage yawan yan takara domin samarwa masu zabe dama jam,iyya sauki wajen samun dan takara mai inganci Wanda kuma ya cancanta zai kuma iya cin zabe.
Tabbas rage yawan yan takara zuwa 4 ko 6 wani mataki ne shima dake cikin tsarin zabe, yana karfafa jam,iyya ya kuma bata karfin tsayawa da kafafunta. Haka ma fito da dan takara gamayya guda daya shine mafi a,a,la a jam,iyya shine kuma zai kawarda hargitsin da ke biyo baya wajen zaben fidda gwani, ya kara hada kan yan jam,iyya tareda da kaiwa ga nasara.
Wannan wata manuniyace dake nuni da cewa duk wani ko wata yan jam, iyya dakeda burin ganin jam,iyya taci zabe ya kamata ya kawarda ra,ayi ko sonkai wajen goyon bayan hukuncinda iyayen jam,iyyar suka yanke wajen fittarda dan takara domin samun nasara da kuma alfanu ga jaharmu ta Edo.
Mohammed Bello Doka ya fassara.
Tags
Hausa