Dr. Mrs. Mary Alile tayi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwa

Shugabar matan jam,iyyar APC kuma shugabar kungiyar nan mai fafutukar kare haqqin mata da qananan yara wato Dr. Mrs. Mary Alile tayi bikin zagayowar haihuwa tare da yan uwa da abokan arziki a gidanta dake babban birnin tarayya Abuja. 

Dr. Mary Alile ta samu sakonnin taya murnar wannan muhimmiyar rana daga sassa dabban dabban na duniya, wannan wata manuniya ce ga irin karbuwarda shugabar matan ta samu daga ciki da wajen jam,iyyar. 

Masu hange da tsokaci akan harkokin siyasa sun kuma yabawa Dr. Mary irin yadda ta yaki zuciyarta ta kuma kawarda al,mubazzaranci a wannan bikin sabanin yadda shuwagabanni ke wulakantarda dukiya wajen ire iren wannan bikin. 

Wani mai sharhi a jaridar Abuja Network News yayi nuni irin yadda Dr. Mary ta yi bikin cikin ruwan sanyi a gidanta batare da wawura da kuma bata dukiyar al,umma ba, ita kanta mawallafiyar jaridar Abuja 24 Hajiya Fatima Sambo tace tabbas wannan abun a yaba ne. 

A halin yanzu dai masu ruwa da tsaki daga sassa dabban dabban na duniya naci gaba da aiko sakonnin taya murna da san barka ga shugabar matan kuma shugabar kungiyar Sister to Sister Worldwide. 

Kawo yanzu sama da masu mulki 100 ne suka aiko da sakonnin taya murnar da sambarka. Tabbas wannan wata manuniya ce ga irin karbuwar da shugabar matan ta samu a ciki da wajen jam, iyyar sabanin wudanda suka rike irin wannan mukamin daga a baya.

Kadan daga cikin wudanda suka aiko da sakonnin taya murnar sun hada da,  Hon. Ehiozuwa Johnson Agbonayinma dan takarar Gwamnan jahar Edo, Mr. Pius Alile shugaban kungiyar Pius Alile Coalition, Hon. Victoria Omua Amu, Supreme Vision Brothers, Sister to Sister Worldwide, Engr. Lawrence Osarobo Okah da sauransu.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post