Shugabar matan Jam,iyyar APC ta kasa ta sake samun lambar yabo a matsayin Jarumar Mata yan siyasa na kasa shekarar 2023. An karramata da wannan lambar yabon ne a wani gagarumin taro da kungiyar *Leadership and Development Award* da aka gudanar a birnin Benin dake jahar Edo.
A matsayinta na shugabar matan jam,iyyar APC ta kasa Dr. Mrs. Mary Alile na ci gaba da daukar hankulan mutane duba da irin namijin kokarinda takeyi wajen kawo wa jam,iyyar nasara a fannoni dabban dabban.
Wannan lambar yabon wata manuniya ce ga irin muhimmiyar rawarda mata ke takawa wajen ci gaban al,umma dama kasa baki daya. Dr. Mrs. Mary Alile ta zamo jigo a wannan bangaren.
Shugabar zantarwar kungiyarda Dr. Mrs. Mary Alile ta kirkira ne ta Sister to Sister reshen Najeriya Mrs. Rachel Edoba ne ta karbi wannan lambar yabo a madadin Dr. Mary.
*CAPACITY MEDIA HAUSA*