Dr. Mary Allie ta Taya Jarret Tenebe Murnar Samun Kujerar Ciyaman na Rikon Kwarya a Edo

Shugabar matan jam,iyyar APC Dr. Mrs. Mary Alile ta taya sabon ciyaman na rikon kwarya a jam,iyyar APC  na jahar Edo Mr. Jarret Tenebe murnar samun wannan mukami. 

Mrs. Mary  a wata sanarwa ta musamman da sakawa hannu tace wannan yunkurin wani abun a yaba ne a kuma yiwa jam,iyyar murna a jahar ta Edo duba da irin namijin kokarinda Mr. Jerret keyi wajen kawo cigaba a jam,iyyar. 

"Ina taya Mr. Jarret murnar samun wannan mukami na ciyaman din jam,iyyar APC a jahar Edo na rikon kwarya, ina kuma yi masa fatan alkhairi shi da jahar ta Edo." Dr. Mary ta rubuta. 

" jajircewarka da kuma sadaukarwarka ne ya janyo hakan, ina kuma yi maka fatan alkhairi da adduar nasara." Ta kara da cewa. 

Dr. Mary ta kara da cewa Mr. Jarret zai bukaci yin aiki tukuru wajen ganin ya hada kan yan jam,iyya tare kuma da sasanta sassa da kyautata mu,amala tabbas wannan ne kawai zai kawowa jam,iyya da jaha ci gaba. 

Daga karshe Dr. Mary tayi kira ga Mr. Jarret daya dage damtse wajen kwato jahar Edo daga halin da ta Shiga a hannun jam,iyyar APC a cikin shekaru 8 da suka gabata. 

📷 CAPACITY MEDIA HAUSA

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post