Dole Mu Yaki Mulkin Kama Karya a Edo, Mu Kuma Sabunta Zato- Dr. Mrs. Mary Alile

By Mohammed Bello Doka

A daidai lokacinda ake ci gaba da matsa kaimi domin zabar sabon  Gwamnan jahar Edo, tattare da hauragiya, hayaniya da kuma cakwakiya da aka saba yanada matukar muhimmanci muyi tunani mu kuma tantance Wanda zamu zaba a matsayin Gwamnan jahar tamu ta Edo. 

Yana da muhimmanci mu fahumci cewa yin kuskure wajen zaben Wanda bai cancanta ba zai kara jefa jahar cikin halin waini yasu. Tabbas yanada muhimmanci mu maida hankali wajen zaben Wanda ya cancanta, ya dace yake kuma da sanin makaman aiki. 

A wata sanarwa ta musamman wacce shugabar matan jam,iyyar APC ta kasa Dr , Mrs, Mary Alile ta sakawa hannu tana cewa " Jahar mu ta Edo ta shafe shekaru cikin halin kakanikayi sakamakon mulkin kama karya, handama da babakere Wanda yasa abubuwa suka tabarbare komai ya lalace tareda tambadewa, dole ne mu mike tsaye mu yaki wannan shiriritar mu kuma Sabunta Zato na alkhairi. 

A bisa wannan maudu,in ne yan jahar ta Edo suke bukatar samun Gwamna na gari, mai fahimta, sanin ya kamata dama sanin makamar aiki, dole ne mu kwato Edo daga hannun yan baranda mu sabunta zaton al,umma. 

 *📷CAPACITY MEDIA HAUSA*

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post