Ku Guji Amfani da Irin Wannan Tumatir din Domin Gujewa Ciwon Daji ( Cancer)

A yayin da kuka je kasuwa domin siyayya, a lokacin da kuke kokarin takaita kuɗin da za ku kashe, kar ku yarda saboda neman sauƙi ku siya tumatur irin waɗan nan. 

Akwai wata ƙwayar halitta mai suna ASPERGILLUS FLAVUS a cikin ruɓaɓɓun tumatur dake fitar da wani nau'in sinadari mai cutarwa da ake ce ma AFLATOXIN.

Shi wannan AFLATOXIN ɗin an tabbatar da yana haifar da ciwon Daji Na Hanta (Liver Cancer).  Ba'a rana ɗaya abin ke faruwa ba, a hankali a hankali zai dinga ginuwa a jiki. Shi wannan AFLATOXIN ɗin zafin wutar da ake dafa abinci yau da kullum baya kashe shi, yana iya rayuwa CIKIN MATSANANCIN ZAFI/WUTA.

Abin takaici dai shi ne, ƙasar mu ba tayi cigaban da za'a dinga sa Ma'aikatan Lafiya na musamman suna zagaya kasuwanni domin tabbatar da ingancin abubuwan ci da muke siya ba. Kowa na iya siyar da abinda ya ga dama.

Ku lura sosai da wanda suke ɗauke da abu kamar YANAR GIZO a jikin su, duk rintsi kar su samu wajen shiga a wajen ku, ku guje musu da gudu.

Allah Ya cigaba da bamu kariyarSa, Ameen. 

 *Dr Isham

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post