Ganawar ta gabata ne a ranar Talata 7 ga watan Disamba, 2023, a birnin Birmingham dake kasar ta Ingila.
Tawagar shugabar matan ta jam,iyyar APC wato Dr. Mary Alile ta hada da shugaban (PACI) Mr. Pius Alile, Mr. Erica Subuloye, mai taimakawa ofishin shugabar matan akan harkokin ketare, Alhaji Yusuf Abdullahi, shugaban kungiyar yan asalin jahar Edo a birnin na Birmingham, Hon. Edo Aguebor tsohon babban mai taimakawa Gwamnan jahar Edo , Godwin Obaseki; da sauransu.
Wanda ya jagoranci tattaunawar Hon. Edo Aguebor ya fara da bayani akan muhimmanci kafafen sada zumunta wajen yada manufa da kuma irin gudun mawarda yayan jam,iyyar ta APC mazauna kasashen waje zasu iya bayarwa wajen ganin jam,iyyar tayi nasara a zaben jahar Edo dake zuwa a 2024.
A nashi jawabi yayi tsokaci ne akan yadda yayan jam,iyyar zasu iya hada karfi da karfe wajen cimma manufa, musamman dangane da zaben mai zuwa a jahar Edo.
Ita kuwa shugabar matana a nata jawabin tayi kirane ga yayan jam,iyyar da su bada gudun mawa na musamman akan cimma kudurin sabunta zato ( Renewed Hope) na gwamnatin mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ta kara bada shawara ga mazauna kasashen wajen yan Najeriya dasu kara maida hankali wajen al,amurran siyasa da kuma bada gudumawa wajen gina jam,iyya da tabbatarda nasara. Daga karshe ta kuma yi gargadi akan kokari ko yunkurin raba kawunan yayan jam,iyyar a wajen kasar Najeriya.
Daga karshe shugabar matan ta jam,iyyar APC wadda ta cika kwanaki 100 akan karagar mulki ranar litinin 4 ga Satan Disamba batayi kasa a guiwaba wajen mika godiya da sa albarka ga shugaban jam,iyyar ta APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje akan irin gudun mawarda yake bawa yayan majalisar zartarwar jam,iyyar domin yada manufa.
CAPACITY MEDIA HAUSA