Wani baki na musamman daya samu halattar masu hannu da shuni daga sassa dabban dabban na kasar nan shine taron bikin Fatima Isah da angonta Idris Akanbi wanda aka gudanar a babban birnin tarayya.
Capacity Media ta hango Dr. Mrs. Mary Alile tareda masu bikin, yan uwa da abokan arziki ana sakata ana walawa tareda daukar hotuna cikin annashuwa.
Taron ya samu halattar matar shugaban majalisar dattawa na kasa wato Ekaette Akpabio da Senator Grace Folasade dama matan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma tsohon dan takarar shugaban kasar wato Alhaji Atiku Abubakar. Haka ma mandate sakatare ta Abuja Mrs. Adedayo Michael da mukarrabanta sun samu halattar taron.
A lokacinda take zantawa da yan Jaridan CAPACITY MEDIA Dr. Mary Alile tayiwa ma,auratan adduar zama lafiya da zuri,a dayyaba.
*CAPACITY MEDIA HAUSA*