Mataimakiya ta Musamman a Ofishin Shubagar Matan Jam,iyyar APC ta bada Tallafin Kiwon Lafiya a Akure

A daidai wannan lokacin na karshen shekara da ake bukukuwa tareda bada kyaututuka domin murnar zagayowar karshen shekarar. Babbar mataimakiya ta musaamman a ofishin Dr. Mary Alile Erica Subuloye ta bada gudumawa ta musamman ta kiwon lafiya ga gajiyayyu a Lakeview Medical Center dake Akure, jahar Ondo. 

Wannan wata manuniya ce ga irin tarbiyyarda shugabar matan me baiwa masu aiki tareda ita. Wannan yunkurin ya kuma karawa bukukuwan karshen shekarar armashi musamman a garin na Akure. 

Wannan kokarin na Erica Sobuloye wata manuniya ce ga irin mutanenda Dr. Mary ta zagaye kanta dasu, da kuma irin manufar alkhairi da suke yadawa. 

A nata bangaren shugabar matan ta yabawa kokarin Lady Erica wajen taimakawa gajiyayyu ta kuma yi kira ga sauran masu riko da madafun iko dasu dage damtse wajen taimakawa gajiyayyu a fadin kasar.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post