Dr. Mary Alile ta Mika Sakon Ta,aziyya ga Jahohin Plateau da Taraba

Shugabar matan jam,iyyar APC ta kasa Dr. Mrs. Mary Alile ta mika sakon ta,aziyya ga mutanenda harin rikicin manoma da makiyaya ya rutsa dasu a jahohin Plateau da Taraba ana gab da fara bukukuwan kirsimati. 

Dr. Mary tayi Allah wadai da irin wannan kisan gillan mai cike da ban tausayi da rashin imani, Dr. Mary tace tanada yakinin Gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bazatayi kasa a kafa ba har sai tayi maganin tareda hukunta ko suwaye masu wannan mummunan aikin. 

Ta kuma kara da kira ga iyalan wudanda wannan rikicin ya rutsa dasu dacewa su dauki wannan a matsayin wata jarabawa. Ta kuma rokesu da kada su dauki doka a hannunsu amma suyi amfani da kafafen Shari,a domin neman kadin yan uwansu da aka kashe. 

Tabbas Gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bazatayi kasa a guiwa ba wajen ganin an zakulo tareda hukunta duk wani mai hannu a wannan mummunan aiki inji Dr. Mary. 

Daga karshe Dr. Mary ta kara da sake aika ta,aziyya ga yan uwa da Gwamnatin wudannan jahohin da fatan Allah ya basu hakurin jure rashin. 

Sa Hannu. 
 *Dr. Mrs. Mary Alile* 
Shugabar Matan Jam,iyyar APC ta kasa.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post