Dr. Mary Alile ta Mika Godiya ta Musamman ga Wudanda Suka Tayata Murnar Cika Kwanaki 100 a Ofis

Shugabar Matan jam,iyyar APC ta kasa Dr. Mary Alile ta mika godiya ta musamman ga wudanda suka tayata murnar cika kwanaki 100 a matsayin shugabar matan jam,iyya mai mulki ta APC. 

A wata sanarwa data sawa Hannu Dr. Mary na cewa " ina wannan rubutun ne domin mika godiya ta mussamman ga duk wudanda suka tayani murnar cika kwanaki 100 a matsayin shugabar matan jam, iyyar APC ta kasa. Ina matukar farin ciki da  samun  Wannan matsayin, da kuma nauyi da aka dora man. 

Da farko zanso in mika godiya ta musamman ga Dr. Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam,iyya ta kasa da kuma yan majalisar zantarwa ta kasa na jam,iyyar dangane da irin nuna yarda da kuma goyon bayanda suka bani. Ina kuma mika godiya ta musamman ga Hajiya Zainab Ibrahim, mataimakiyata da kuma sauran mataimaka na daga sassa dabban dabban na kasar nan. Ina godiya da yunkuri da himmarku wajen tallafawa mata akan harkoki na yau da kullum. 

Ina kuma amfani da wannan damar domin mika godiya ta ga babban aboki kuma miji na  Hon. Pius Alile akan goyon bayanda ya bani wanda baya misaltuwa. Tabbas goyon bayanka da shawarwari sunyi matukar tasiri ga duk wata nasara dana samu a rayuwa kawo yanzu dama a harkokin siyasa.

Ina kuma alfahari da nasararinda muka samu a wudannan kwanaki 100 na farko a matsayina na shugabar matan jam, iyyar APC ta kasa, da suka hada da kare hakkin mata, baiwa mata damar shiga a siyasa a dama dasu, da kuma fadakarwa, ilmantarwa ta  tallafa musu a kan sabgogi na yau da kullum. 

Ina matukar mika godiya ta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ga irin damarda ya baiwa mata a mulkinshi da kuma irin taimako da goyon baya dayake bamu wajen kare hakkin mata da tallafa masu. Haka kuma ina mika godiya ta musamman ga maidakinsa Sanata Oluremi Tinubu kan irin namijin kokarinda take wajen taimakawa, tare kuma da kula da bukatun mata na musamman. Wannan abun a yaba ne. 

Ina kuma mika godiya ta musamman ga masu ruwa da tsaki daga sassa dabban dabban da suka zo muka hada karfi da karfe wajen kare hakkin mata, tallafawa, ilmantarwa dama samarda abun yi da matsuguni ga mata a duk fadin kasar nan, ina maku fatan alkhairi. 

Sannan duk wannan ci gaban da muka samu ba Abu bane da zai yiyu ba tare da taimakon dinbin ma,aikata na ba, tabbas taimakonku na kara man kwarin guiwa, yana kuma rage man aiki tare da taimaka man wajen sauke wannan nauyi daya rataya a wuyana. Ina kuma da yakinin cewa zamu ci gaba da aiki tare wajen cimma manufa da kuma gagaruman nasarori. 

A daidai wannan lokacin da nake duba akan kwanaki 100 na farko a wannan mukamin tabbas wannan bawai taron taya murna bane kawai, a,a wani nuni ne ga irin namijin kokarinda mukayi dukkanmu wajen cimma nasara. 

Daga karshe ina mika godiya ta musamman ga kungiyoyin mata masu zaman Kansu akan irin gudun mawa da kuma goyon bayanda suka bani domin samun wannan matsayin da kuma wudannan nasarori da muke tunawa a yau. 

Sa Hannu. 
Dr. Mrs. Mary Idele Alile
Shugabar Matan Jam,iyyar APC ta Kasa.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post