Sister-to-Sister Ta Gudanarda Binciken Lafiyar Gajiyayyu da Bada Tallafin Kayan Masarufi

CAPACITY MEDIA HAUSA 

Kungiyar nan mai taken sister to sister world wide wadda shugabar matan jam,iyyar APC ta kasa ke jagoranta wato Dr. Mrs. Mary Alile ta gudanarda binciken lafiyar gajiyayyu maza da mata tare kuma da basu tallafin abinci da wasu kayan more rayuwa. 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacinda kungiyar ke bikin cika shekaru 7 da kafuwa, gobe 24 ga watan Nuwanban 2023. Wannan taron ya samu hallarar manyan baki daga sassa dabban dabban na kasar nan dama wajen Najeriya. 

An kafa kungiyar ne a shekarar 2016. Tana da rassa a Nahiyoyi hudu (4) na duniya, kasashe bakwai (7) na duniya da kuma jahohi tara (9) na Najeriya. 

Kungiyar sister to sister ta bada gudunmawa sosai wajen taimakawa mata ta hanyoyi dabban dabban da suka kunshi sanin makaman aiki, samarda sana,a da kuma bada tallafin gaggawa. Wannan duk cikin kokarin Dr. Mrs. Mary Alile ne. 

📷 CAPACITY MEDIA HAUSA

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post