Shugabar Matan Jam,iyyar APC ta kasa kuma shugabar kungiyar "Sister-Sister World Wide" wato "daga yar uwa zuwa ga yar uwa a duk fadin duniya", Dr. Mrs. Mary Alile ta sauka birnin Benin dake jahar Edo wajen bikin cika shekaru 7 na kungiyar mai zimmar taimakawa mata da kananan yara.
Tare da ita akwai babbar mai taimaka mata a mazabar a tsakiya da kuma babbar mai kula da tsarin aiki a mazabar.
Dr. Mrs. Mary Alile itace sanye da gilashi. Wannan taron zai kasance wani sabon mabudin jerin tsare tsaren da kungiyar ta shirya domin fito da hanyoyin taimakawa mata da kananan yara a duk fadin duniya.
Ku kasance tare da Abuja Network News domin cikakken bayani akan wannan gagarumin taron.