Shugabar Matan Jam,iyyar APC ta kasa Dr. Mrs. Mary Alile ta kai Ziyarar ban girma ga Mahaifiyar Oshiomole

Lahadi 25, ga watan Nuwanba, 2023, shugabar matan jam,iyyar APC ta kasa ta kai Ziyarar ban girma ga Mahaifiyar tsohon Gwamnan jahar Edo, tsohon shugan jam,iyyar APC ta kasa kuma Sanata mai ci yanzu Mr. Adam Oshiomole.

Wannan Ziyarar ta samu halattar kungiyoyin mata daban daban daga mazabar Edo ta Arewa, da kuma ciyaman na jam, iyyar ta APC a karamar hukumar mulki ta Orhiomwon Mr. Julius Agbonze da Mahaifiyar shugabar matan ta wato Mrs. Eunice Ateru zuwa gidan Hajiya Aishatu Oshiomole Mahaifiyar shi Adams Oshiomolen.

Hajiya Aishatu tayi lale marhaban da zuwan bakin nata inda ta tarbesu cikin murna da annashuwa, ta kumayi matukar yabawa kokarinda Dr. Mrs. Mary keyi wajen taimakawa marasa karfi tare da gajiyayyu a duk fadin kasar nan inda tace wannan namijin kokarin abun a yaba ne. 

Hajiya Aishatu ta kuma bada labarin irin dawainiyarda ta sha wajen taimakawa danta wato Adam Oshiomole daga fara Shiga shiyasarshi da yadda suka yita fama har gashi yau Allah ya kaishi makula a harkar siyasa a Najeriya. Ta kuma yiwa Dr. Mrs. Mary Alile adduar Allah ya daukakata ita ma takai wannan matsayi a matsayinta na wakiliyar mata. 

A nata jawabin Dr. Mrs. Mary Alile ta yabawa Hajiya Aishatu Oshiomole akan irin gudunmawarda take bayarwa akan harkokin siyasa a jahar ta Edo da kuma irin namijin kokarinta wajen taimakawa danta Adam Oshiomole. Ta kuma roki Allah daya cigaba da taimaka mata wajen dauke wannan nauyi. 

Bayan bayanai da jawabai matan jam,iyyar da suka samu halattar taron sun baje sun kuma sakata sun wala da kade kade da raye raye hadi da makulashe. 

CAPACITY MEDIA HAUSA.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post