Femi Fani Kayode Ba Makiyin Arewa da Musulmai Bane

Muhammad Bello Doka 

Sadaukin Shinkafi Cif Femi Fani Kayode ya tsinci kanshi   atsaka Mai wuya a kafafen sada zumunta na cikin gida dana waje. wasu sassan sada zumuntar sunyi kokarin sai sun Yi masa kazafin shi makiyin Al ummar Arewa ne da Addinin musulunci Baki daya. Wannan shi yajanyo Cece kuce a tsakanin Al umma.  

Kai tsaye a kokarin Maida martanin wannan kazafi, Idan akayi la,akari tareda  duba mai karatu zai gane dangantakar dake tsakanin me girma Fani Kayode da sarakunanmu na gargajiya inda ya samo asalin sarautarsa ta Sadaukin Shinkafi, wannan shi ya tilasta min wayar da kan jamaa  dangantakar da alummar yankin Arewa. da asalin  dangantashi da akeyi a makiyin Arewa da musulmi.                                                       
Yana daga cikin muhimman abubuwan daya kamata  mutane su fahimta samun sarauta irin wannan sannan a yankin Arewa fadar mai martaba Sarkin Gabas na Shinkafi Wanda ke karkashin masarautar mai alfarma Sarkin musulmin daular Usmaniyya ba kowanne mutum ke da damar samun Hakan ba sai Wanda ya cancanta.

Bari muyi tsokaci akan  abinda yasa naki in aminta da wancan kazafi da ake wa Fani Kayode na cewa shi makiyin Arewa ne da musulunci,  shin idan shi makiyin Arewa ne me yasa zai karbi sarautar data fito daga yankin Arewa karkashin mulkin musulunci na Shinkafi? In har yakasance yanada kulli akan Yan Arewa da musulunci?                    
Awani Karin hasken, Fani Kayode ya kasance ya sadaukar da lokacinshi da karfinshi  hadi da dukiyarsa don ganin cigaban wannan masarauta karkashin daular musulunci ta bunkasa. Tare Da kula da dukkan  Wani Mai mukami akarkashin wannan masarautar. Sannan a duk inda yake yana alfahari da wannan mukami na sadaukin Shinkafi.
                                                                        Tambaya anan, shin idan  Fani Kayode makiyin Arewa ne da musulunci, tayaya zai goyi bayan Muslim Muslim ticket? Alokacin da kabilanci da rabe rabe addini  yayi tasiri a cikin kasar, tabbas ya jajirce  don ganin Tinubu Shettima sunyi nasara a zaben daya gudana wanda har yanzu babban mai goyon  bayan wannan gwamnati  mai ci ne.

Bugu da Kari  Fani Kayode mutum ne Wanda yayi fice wurin goyawa manyan yan siyasar Arewacin kasar nan baya   kamar su Mai mala Buni, Bello matawalle, kashim Shettima, da sauran manyan fitattun Yankin Arewa. 

Nuna goyon bayanshi ga rikicin dake gudana a Falasdinu, tare da nuna kin jinin isra ilawa akan kisan kiyashin da Falastinu ke fuskanta a wurin isra,ilawa yan kama wuri zauna tabbas abin ayaba mishi ne.               
Jajircewar Fani Kayode da yunkurin fito da gaskiya da tsageta akan masu mulki  shi ya janyo mishi bakin jini da tarin makiya , duk da hakan baisa ya canja daga abunda aka sanshi akaiba na gaskiya tareda  aiki da ita.  Mu hadu a kashi na biyu. 

Fassara Fatima Hussain Muhammad  Abuja Network News .

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post