Jarumin Matashinda Ya Ceci Rayuwar Musulmi Da Yawa A Borno.

Shekaru 6 da rasuwar jarumin matashi wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga musulmai da dama a cikin masallacin Maiduguri.

Tarihin yakin Boko haram ba zai taba cika ba inhar ba'a sanya sunan Matashi Yakubu Fannami ciki ba.

Yakubu Fannami, dan makarantar Sakandare (SS1) ya nuna jaruntarsa a lokacin da wata yar kunar Bakin wake tayi yunkurin kutsawa masallaci yayinda ake salla a Kaleri dake jihar Borno.

Yakubu Fannami,  yayi kukan kura ya rungumi yar kunar bakin waken kafun takai ga shiga masallacin, domin rage asarar rayukan masallata da zata dauka a masallacin.

Yakubu ya gwammaci shi da ita su mutu maimakon dumbin masallatan dake cikin masallacin su mutu, inda nan take ya turmushe yar kunar bakin waken a kasa kafun daga bisani Bom din dake jikinta ya tarwatse da su.

Allah jikan Yakubu Fannami,

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post