Hadarin Dogara Da Labarun Turawa Ko Harshen Su 2 Na Mallam Ibrahim Bature

Mallam Samaila Usman Dan Asalin Jihar Yoben Nigeria ne, yana gab da kammala Digirin Digir (Ph. D) a nan Kasar Sin.

Sadda Professor dinsa a aminche ta dauke shi a matsayin dalibi, tayi hakan ne bisa ga kasada, sabida yadda Ranking na kasashen turawa ya maida Jami'ion mu na Nigeria koma baya, idan ka shiga baka ganin wasu ma.

Amman yanzun Da kanta ta sanar da Malamina (Supervisor) cewa bata taba samun dalibi Mai hazaka da kwazon Samaila ba tunda ta fara koyarwar a nan kusan Shekaru Ashirin. 

Professor dina ya sanar dani da Samaila haka bayan da yazo yayi wani binchike a Laboratory namu.

Ta sanar da Malamina bayan data nemi alfarmar Samaila zaizo yayi wani aiki wajen mu, Inda shima ya sanar da ita ya samu dalibi daga Nigeria shima (ni kenan).

Dalilin Samaila yanzun haka Malamar tasa wadda tana cikin manyan masana a Kasar Sin, Inda har ta Samu lambar yabo a Kasar, Ta aminche da wani abokina Wanda nasa yayi mata email, Don kawai taga Dan Nigeria ne, har an bashi gurbin karatu, In Shaa Allah September 2023 zai Jona mu a nan. 

Samaila yayi Degree na Farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi, Yayi Degree na biyu a Jami'ar Noma dake Abekuta. Yana kwarewa a bangaren ilimi bunkasa chiyawa (Pasture and Range Management).

Kunga da ta biye wa wallafar turawa dake maida Jami'oin mu baya, da bata dauki Samaila ba. Sannan irin hazaka da Samaila ya nuna, yasa muma dole mu kara dagewa, Don samar wa Kasar mu suna da Daraja a duniya.

Dukda haka, ina kira Ga Gwamnatin Nigeria ta kara samar da kayan aiki, ta gyara aikin mu da malanta, Don samarwa Makarantun Nigeria muhimmanchi a idon duniya.

Muna alfahari da ilimin gurguzu da muka samu a Nigeria dukda kasan cewar babu kayan aiki a Makarantun da mukayi, yawan chi practical a Littafin ake koya Mana.

Naku,
Malam Ibrahim Bature.

Barkan mu da shan ruwa.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post