Hadarin Dogara Da Labaran Turawa ko Hasashen su 1 By Mallam Ibrahim Bature


Dazu bayan mun dawo Sallar La'asar, wani Musulmin Sin ya tsayar dani, Yake ce mani daga wace kasa nazo, Nace Mishi Nigeria, neighbour dina kuma yace mishi Pakistan, yace eh, yasan Pakistan duk Musulman ne, Amman bai taba tunanin bakar fata akwai musulmai ba, sabida yawan chi yasan duk Kiristochi ne.

Sadda Yake mamakin, baisan ni nafi shi mamaki ba, sadda nazo wani masallachi Mai kimanin chin mutum 3000 zuwa 4000 nazo Sallar Juma' a farkon zuwana naga Yan Kasar Sin Musulmai sun chika duka benayen masallachin ba.

Na tuna kafin nazo yadda tashohsin turawa ke nuna Kasar Sin a wani waje da musulmi baya da yanchi, ko katabus.

Sai gashi kusada Makarantar mu akwai masallatai ukku, biyu daga cikin ukkun Duk Katsina State ba masallachi Mai Girman su, na ukkun shine zan iya hada Girman sa da masallachin Komashi dake Katsina.

Barkan mu da shan ruwa,
Azumi na Ukku yau.
Allah ya amsa Mana bukatun mu na alkhairi, Amin.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post