Me Yasa Atiku Abubakar Ke Alfahari Da Adawarsa Da Shari,ar Musulunci?

Wato shidai mutum idan musulmi na gari ne to dole ne yayi murna idan yaji ance an kaddamarda Shari,ar musulunci a wani bangare koda kuwa ba wajenda ya shafe shi bane. 

Haka kuma duk musulmi na kwarai idan yaji ance an kaddamar ko za,a kaddamarda Shari, ar musulunci a wani waje to ya kamata yayiwa wannan wajen fata na gari ya kuma yiwa masu wannan yunkurin fatan nasara. 

Amma abunda ke bani mamaki shine tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar baya jin kunyar nuna adawarsa da Shari'ar ta musulunci. Bama wai nuna adawarba abun har yakai ga alfahari da bugun gaba a kafafen yada labarai. 

A shekarun baya an kawo rahotannin yadda Atiku ke gayawa wani gidan jarida a Faransa cewa a shekarar 1999 a cikin manyan yan siyasan arewacin Najeriya shi kadai ne yayi Adawa da kaddamarda Shari, ar musulunci a wancan lokacin.

Wannan abun yayi matukar bata wa musulmi rai a fadin duniya inda mutane daga sassa dabban dabban na duniya suka ringa sukar lamirin na Atiku tareda masa raddi. 

Mutum zaiyi tsammanin cewa Atiku ya koyi wani abu daga wannan tabargaza tashi. Na kira hakan tabargaza domin kuwa a musulunci ance koda mutum yana laifi ko yayi laifin to da banbanci idan yana kokarin boye wannan laifin baya son mutane su sani, amma laifi mafi muni shine mutum ya ringa nunawa duniya koma ya ringa alfahari da shi. 

Kwatsam kuma yan kwanaki kalilan da suka wuce saiga Atiku Abubakar ya sake fitowa a gidan talabijin na channels yana alfahari da bugun gaba akan cewa ai ya fada ba inda Shari,ar musulunci zata kai a Najeriya, harda tambaya cikin izgili to yanzu ina Shari'ar take? Wa,iyazu billah.

Jama,a wudannan sunefa manyan mu, sune shuwagabannin mu da muke duban cewa zasu kare mana addinin mu da al,adarmu sune wakilanmu da yakamata ace muna alfahari dasu. 

Abun tambaya anan shin a irin wannan halin idan Atiku Abubakar ya samu dama shin zai karfafa Shari'a,r musulunci ne ko zai daqile ta?

Mai karatu sai kayi amfani da baiwa da hikimarda Allah ya baka kayiwa kanka hukunci.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post