Ganin yanda samar da sabbin kudi da soke amfani da tsoffi ya jawo matsaloli da yawa a cikin al’umma, daga talakawa da attajirai da yankasuwa, dantakarar Jam’iyyar APC ya yi alkawari, sabanin dantakarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da Peter Obi wadanda suke murna da wannan mummunan tsari da zai talauta al’umma, idan aka zabi ALHAJI AHMED BOLA TINUBU, a take zai gyara wannan tsarin ta yanda ba wanda zai yi asarar kudinsa kuma mutane za su ci gaba da hadahadarsu ta kudi yanda suka saba a tuntuni.
1. Na farko za a buga wadatattun kudi da jama’a suke bukata a harkar kasuwancinsu.
2. Na biyu, za a ci gaba da amfani da duk tsoffin kudi har karshen shekarar nan, da ta Naira dubu, da ta dari biyar da ta dari biyu.
3. Na uku duk wanda yake da tsoffin kudi za a karba a ba shi sabbi idan ya kawo kome jimawa a nan gaba.
4. Na hudu, mutane za a ba su damar yin kasuwancinsu nak’adan kamar yanda suka saba, ko ta hanyar transifa, ko ta banki, ba tare da takurawa ba, musamman la’akari da cewa a jihohi da yawa na kasar nan, akwai kananan hukumomi da yawa da ba su da bankuna kwata-kwata ko kuma bankunan basu wuce daya tak ba. Akwai kuma wurare da basu da sabis da za a yi tiransifa ko kuma ba ko yaushe ake samun sabis din ba.
5. Na biyar, za a kara yawan masu POS da bunkasa sana’arsu don su rika samar da isassun tsabar kudi wa jama’a.
6. Na shida, za a wadata kananan hukumomi da bankuna da wuraren ajiye kudi saboda amfanin mutanen karkara.
Wannan tsari na Ahmed Bola Tinubu zai fid da mutane daga cikin halin ha’ula’I da wannan canjin sabon kudin ya kawo musu.
Jama’a kar ku yarda ku zabi wadanda suke murna da wannan halin takurawa da kuke ciki. In kun zabe su za su ci gaba da gasa muku aya a hannu. In kunne ya ji, jiki ya tsira. Ku zabi dantakarar jam’iyyar APC, Alhaji AHMED BOLA TINUBU, don walwalarku, da bunkasa tattalin arzikinku, da hadin kan kasa da kawo cigaba.
———————
Wannan sako ne daga helkwatar kampen ta Alhaji Ahmed Bola Tinubu, Jagaban Borgu, dantakarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
——————
APC Presidential Campaign Council
Herbert Macaulay Way
Central Business District, Abuja
17 Fabrairu 2023
————-
Tags
Hausa